Ko Super Eagles za ta koma kan ganiya a neman shiga kofin duniya?

Asalin hoton, Getty Images
Magoya baya da masu sharhin tamaula na caccakar Najeriya, bayan da ta fara wasannin neman shiga gasar kofin duniya ta 2026, wadda ake tsoron da kyar idan Super Eagles za ta samu gurbi, kamar yadda ta kasa zuwa a 2022 a Qatar.
Najeriya ta tashi 1-1 a gida da Lesotho a wasan farko a rukuni na uku, sannan ta kara tashi 1-1 da Zimbabwe a wasa na biyu a cikin rukuni a Rwanda.
Ana ta sukar koci, Jose Pesseiro da kasa morar tarin masu cin kwallo da Super Eagles da take da su, sai dai tsohon dan wasan Najeriya, Peter Rufa'i ya yi kira ga magoya baya da kada su cire tsammani a tawagar.
''Za su iya bamu mamaki. Kwallon kafa wasa ne mara kangado. Ina da tabbaci za su iya komawa kan ganiya, su kuma faranta mana rai.''
Super Eagles tana ta uku a rukuni na uku da tazarar maki biyu tsakaninta da Rwanda ta biyu, wadda ta doke Afirka ta Kudu 2-1 ranar Talata.
Najeriya ba ta samu damar shiga gasar kofin duniya ba da aka yi a 2022, bayan da ta kasa cin Ghana, wadda ita ce ta wakilci Afirka.
Pesseiro tare da tawagar Najeriya suna tare da tarin matsalolin da ya kamata su shawo kai a gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a fara daga 13 ga watan Janairun 2024.

Asalin hoton, BBC Sport
Kawo yanzu Rwanda ce ta daya a rukuni na uku da maki hudu, sai Afirka ta Kudu da maki uku, yayin da Najeriya da Lesotho da Zimbabwe kowacce tana da maki bibiyu da kuma Benin mai maki daya kwal.
Za a ci gaba da wasannin cikin watan Yunin 2024 na neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Amurka da Canada da Mexico a 2026.
Ko da wata matsala a tawagar Super Eagles?
Tun bayan da Pesseiro ya karbi aiki a 2022, ya yi nasarar cin wasa shida aka doke shi a shida daga 15 da ya ja ragama kawo yanzu.
Super Eagles ta ci kwallo 31 - 10 daga ciki ta zura a ragar Sao Tome - an kuma ci Najeriya kwallo 21.
Dan kasar Portugal din ya kai Najeriya gasar cin kofin Afirka da za a yi a Ivory Coast a 2024, wadda wasa daya aka doke ta a cikin rukuni shi ne na Guinea-Bissau.
Bayan da Najeriya ta kasa doke Lesotho da Zimbabwe, tuni ana ta caccakar tsohon kociyan Sporting Lisbon da kuma Porto.
Ta ina Najeriya za ta kara bunkasa kanta?

Asalin hoton, Getty Images
Najeriya ita ce ta shida a jerin wadanda ke kan gaba a taka leda a Afirka ta 40 a duniya.
Burin da ake a kan Najeriya kan samun sakamako mai kyau yana da yawa, bayan da kasar take da tarin 'yan wasa masu cin kwallaye da ke taka rawar gani a Turai.
Cikin 'yan wasan sun hada da Victor Osimhen na Napoli da Victor Boniface na Bayer Leverkusen da Taiwo Awoniyi na Nottingham Forest da Ademola Lookman, wanda ke taka leda a Serie A da Atalanta, ya kamata ace Super Eagles ta sharara kwallaye da yawa a ragar Lesotho da Zimbabwe.
Har yanzu an kasa samun dan wasan da zai maye gurbin John Mikel Obi, wanda ya yi ritaya.
Matsalar masu tsaron raga

Asalin hoton, Getty Images
Francis Uzoho ya yi tashi ya bi kwallo a sama domin tarewa kada ta fada raga, amma bai samu hakan ba.
Ana ta sukar Francis Uzoho kan kurakuren da yake yawan yi a wasannin Najeriya.
Har yanzu magoya bayan Super Eagles ba su da kwanciyar hankali idan dai Uzoho ne ke tsare raga, wanda suke cewa shi ne ke barin kwallo na shiga ragarsa.
Pesseiro ya goyi bayan golan mai shekara 25, bayan wasan sada zumunta biyu da ta buga a watan jiya.
Uzoho ya sabunta shafinsa na sada zumunta, bayan tashi 1-1 da Zimbabwe ranar Lahadi, inda Zimbabwe ta ci kwallo ta hannun Walter Musona a bugun tazara.
Shima Maduka Okoye ya sha suka, bayan da aka fitar da Najeriya a Quarter finals a 2021 a gasar kofin Afirka da Tunisia ta ci 1-0.
Ko Peseiro zai mayar da Super Eagles kan turba a kofin Afirka?

Asalin hoton, Getty Images
Ana sa ran Victor Osimhen shi ne zai ja ragamar Super Eagles a gasar cin kofin duniya a Janairu, bayan da bai buga wasannin neman shiga gasar kofin duniya ba.
Bayan da Super Eagles ta kasa taka rawar gani a wasa biyun da ta buga, ana fargabar watakila da kyar ne idan za ta yi abin kirki a gasar kofin Afirka a 2024.
Ba wanda ke tsammanin za ta yi abin kirki, sai dai hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta bude kamfen don karkafa gwiwar magoya baya a karawar da za ta yi a Ivory Coast.
Super Eagles tana rukunin farko da ya hada da mai masaukin baki Ivory Coast da Guinea-Bissau da kuma Equatorial Guinea.
Idan har Osimhen ya murmure zai kara karfin gurbin masu cin kwallaye a Super Eagles, wanda shi ne kan gaba a zura kwallaye, inda ya ci kwallo10 a wasannin neman shiga gasar Afirka.
Za a buga gasar kofin duniya a 2026, inda Amurka da Canada da Mexico za su karbi bakuncin wasannin.











