An naɗa Usman Abdallah a matsayin sabon kocin Kano Pillars

...

Asalin hoton, NFF

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta sanar da naɗin tsohon mataimakin kociyan Super Eagles Usman Abdallah a matsayin sabon wanda zai jagoranci tawagar ƴan wasanta.

Sashen yaɗa labarai na kulob ɗin ya sanar da nadin Abdallah a shafinta na dandalin X da safiyar Juma'a.

Sanarwar ta ce :“Mun yi farin cikin sanar da cewa mun cimma yarjejeniya bisa manufa don naɗa Usman Abdallah a matsayin sabon jagoran tawagar ƴan wasan mu. Ku kasance da mu don samun cikakkun bayanai kan kwantiragin da sauran abubuwan da ƙungiyar ta sanya a gaba.”

Abdallah zai maye gurbin Paul Offor, wanda aka sallama wata guda bayan an naɗa shi.

Abdallah ya taɓa lashe kofin gasar NPFL ta Najeriya da Enyimba a shekarar 2019 ya kuma kai wasan kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin CAF confederations Cup.