Netanyahu na son komawa shugabancin Isra'ila

An wallafa

"Shin Netanyahu na son dawowa ne?" Na tambayi wata mai fafutuka daga jam'iyyarsa ta Likud da take warware wata makekiyar fasta a bakin kofar shiga wata kasuwa a Jerusalem ta Mahane Yehuda.

"Eh!" ta ce min, cikin kwarin gwiwa da nishadi, yayin da wani mai wucewa ya daga mata hannu.

Kuri'ar da aka kada ranar Juma'a ta nuna cewa tsoho shugaban Isra'ila mai tsattsauran ra'ai Benjamin Netanyahu zai iya dawowa, kujera daya yake bukata ta ba shi rinjayen komawa kan mukaminsa.

Za a ci gaba da kada kuri'ar a yau Talata, a zabe na biyar da za a yi a kasar cikin kasa da shekara hudu.

Kasar ta fada cikin wata tsaka mai wuyar siyasa tun 2019, yayin da aka tuhumi shugaban kasar mafi dadewa kan mulki da rashawa, zamba cikin aminci da cin amana, wanda duka ya musanta.

An hambarar da Netanyahu daga kujerarsa ne a tsakiyar 2021, yayin da dan siyasa mai tsakatsakin ra'ayi Yair Lapid ya hada wata gamayya ta masu sassaucin ra'ayi da masu tsattsauran ra'ayi da hadin kan jam'iyyun larabawa suka goya masa baya.

Gwamnatin hadakar ba ta yi abin da mutane ke tsammani ba daga gareta, amma a karshe ta rushe a watan Yuni.

Yanzu Mista Lapid na matsayin Firaiministan rikon kwarya ne, babban abokin hamayyarsa Mista Netanyahu na neman shiga ofis a karo na shida.

Abin da ya kara bai wa tsohon firaiminstan farin jini a yayin wannan zabe shi ne wata yarjejeniya da jam'iyyarsa ta Likud ta yi da ta Religious Zionism mai tsattsauran ra'ayi, wadda ke samun karbuwa sosai a cikin mutane.

Shugabaninta, Itamar Ben-Gvir da Bezalel Smotrich, na yawan magana a kan daukakar yahudawa. Kuma shi tsohon firaiministan mabiyinsu ne, a bayyane yake nuna wariyar launinsa, da kuma Meir Kahane mai matsanancin kishin kasa, wanda ma'aikatar cikin gida ta Amurka ta ce kungiyarsa ta 'yan ta'adda ce.

Idan suka yi nasarar kafa sabuwar gwamnatin hadaka, za ta tabbatar da kalubale ga kawayen Isra'ila na duniya.

Cikin masu masu sayayya a kasuwar, akwai masu goyon baya dake da yawa kamar dai wadanda suke tsaye a layin nan.

"Wasu kasashen - a Turai da Amurka - suna kallon lamarin ne kawai ta bangare tattalin arziki,"Tehila wata uwa ta shaida mani,. "Muna bukatar Firaiministan da zai tsayawa kasarmu ta bangaren tsaro. Ina kuma ganin Netanyahu ne zai iya haka."

Yonathan na goyon bayan jam'iyyar Religious Zionism kuma yana da kwarin gwiwa kan zaben.

"Akwai karancin rabuwar kai tsakanin masu tsattsauran ra'ayi a wannan karon".

"Fatana shi ne su gaza nutsuwa ta yadda masu tsattsauran ra'ayi su samu damar kafa gwamnati."