Waiwaye: Ƙaddamar da tsarin karɓar bashi da cin zalin ɗalibai a makaranta

An wallafa

Wannan maƙala ce da ke kawo muku bitar muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi

Tinubu ya ƙaddamar da tsarin karɓar kaya bashi ga ƴan Najeriya

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ƙaddamar da kashin farko na tsarin karɓar bashin kaya ga ƴan ƙasar.

Bayanin hakan na ƙunshe cikin sanarwar da mai bai wa shugaban shawara kan yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya fitar.

Tsarin zai bai wa al'umma damar inganta rayuwarsu ta hanyar samun bashin kayyaki inda za su riƙa biya sannu a hankali tsawon lokaci.

Da tsarin, jama'a na iya sayen gidaje da motoci da samun ilimi da kiwon lafiya ta hanyar bashi, inda za su biya daga baya.

Ƴan sanda na bincike kan makarantar Lead British

Rundunar ƴan sanda a Abuja, babban birnin Najeriya ta ce ta aika tawagar ƙwararrun jami'anta zuwa makarantar Lead British bayan bidiyon yadda wata ɗaliba ke cin zalin ƴar ajinsu ya bazu a shafukan sada zumunta.

Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ta ce rundunar ta san da abin da ya faru kuma tana ɗaukan mataki a kai.

A ranar Litinin ne bidiyon da ke nuna yadda ake cin zalin wata ɗaliba ya karaɗe shafukan sada zumunta lamarin da ya fusata al'ummar Najeriya.

Tuni dai hukumar makarantar ta fitar da sanarwa inda ta nemi yafiyar al'umma da kuma iyayen ɗaliban makarantar sannan ta ce ta soma bincike kan lamarin.

Fursunoni 118 ne suka tsere daga gidan yarin Suleja

A tsakiyar makon ne kuma ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya ruguza wani ɓangare na ginin gidan yarin Sule JA da ke jihar Neja, lamarin da ya yi sanadiyyar guduwar fursunoni kimanin 118.

Mai magana da yawun hukumar gyaran hali ta birnin Tarayya, Adamu Duza, a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis ya ce "sakamakon ruwa kamar da baƙin ƙwarya da ya kwashe awa 24 yana zuba ya lalata wasu sassan gidan yarin inda fursunoni 118 suka tsere."

To sai dai wani jami'in gidan yarin da BBC ta tattauna da shi a ranar Alhamis, ya ce sun samu damar kama fursunonin 10 daga cikin 118 ɗin da suka tsere, inda kuma suke ci gaba da baza komar neman mutum 108.

EFCC ta rufe asusun banki 300 kan canjin kuɗin ƙasashen waje

Shugaban hukumar yaƙi da cinhanci ta EFFC a Najeriya ya ce sun yi nasarar gano wani sabon dandalin canjin kuɗin ƙetare "da ya fi dandalin Binance muni".

Ola Olukoyede ya ƙara da cewa hakan ya sa suka rufe asusun banki 300 bisa umarnin kotu da ke da alaƙa da dandalin, wanda ya ce sunansa "P to P" - ko kuma peer- peer.

"Abin da muka gano shi ne ɗaya daga cikin waɗannan asusun ya yi kasuwancin kuɗi sama da dala biliyan 50 cikin shekara ɗaya ba tare da bankuna sun sani ba, kuma babu wanda ya sani," in ji shi yayin taron manema labarai a yau Talata.

Rundunar 'yansanda ta janye wa Muhuyi jami'ai

Babban sufeton ƴan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya janye ƴan sanda kimanin 40 da ke samar wa hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta jihar Kano tsaro.

Matakin ya zo ne bayan binciken badaƙalar kuɗi da hukumar, ƙarƙashin jagorancin Muhuyi Magaji Rimin Gado take yi kan shugaban jam'iyyar APC ta ƙasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

Jaridar Daily a Najeriya ta ruwaito cewa babban sufeton ƴan sandan ya bayar da umarnin janye ƴan sandan ga kwamishinan yan sanda na jihar Kano, Usaini Gumel.

Kodayake daga baya rundunar 'yansandan Kanon ta ce ta yi hakan ne, sakamakon aikin tantance 'yan sanda da ke aiki da hukumar da rundunar ke yi.

Sojin Najeriya sun kashe jagoran 'yan fashin daji a jihar Sokoto

A tsakiyar makon da muke bankwanan da shi ɗin ne kuma rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kashe wani jagoran 'yan fashin daji a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin ƙasar.

Wata sanarwa da ta fitar a shafukanta na intanet ta ce dakarun rundunar da aka tura don yaƙi da ta'addanci ne suka yi nasarar kashe jagoran, wanda ba ta bayyana sunansa ba, a ranar Laraba.

"Bayan samun bayanan sirri, dakaru sun yi wa gungun 'yanta'addan kwanton-ɓauna a wata mashiga da ke ƙauyen Sarma a ƙaramar hukumar Tangaza, inda suka yi nasarar kashe jagoransu tare da ƙwato bindigar AK-47 da kuma babur," in ji sanarwar.