Abin da 'yan Najeriya ke cewa kan cikar kasar shekara 62 da samun 'yanci
Yayin da Najeriya ke cika shekara 62 da samun 'yancin kai, wasu 'yan kasar na cewa ba su san bikin ya zo ba.
Duk da cewa wasu na sukar kasar bisa la'akari da yadda al'amura ke ci gaba da tabarbarewa, misali rashin tsaro da tsadar rayuwa, wasu sun ce an samu ci-gaba ta fuskar ingantar rayuwar mata.
A shekarar 1960 ne Najeriya ta samu 'yancin nata daga Birtaniya. Sai dai da dama daga cikin matasan kasar na cewa 'ba su gani a kasa ba' kasancewar babu wani abu na inganta rayuwarsu da ke faruwa a kasar mai yawan jama'a miliyan 218 a ganinsu.
Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da kasar ke tunkarar babban zaben da za a yi a shekara mai zuwa, 2023.
Tun bayan samun 'yancin kasar, Najeriya ta yi shugabanni 11, inda shida daga ciki suka kasance sojoji sannan biyar farar hula.
Najeriya ce kasa mafi yawan jama'a a nahiyar Afirka amma wadda kuma wasu ke yi wa kallon tana daya daga cikin mafiya koma-baya a nahiyar bisa la'akari da arzikin da Allah ya huwace mata.
Matsalar rashawa da cin hanci ne dai babban kalubalen da kasar ke fuskanta, al'amarin da ya haifar da kusan dukkkannin matsalolin da 'yan kasar ke fama da su.



