Giroud ya zama dan wasan mafi tsufa da ya ci wa Faransa kwallo

An wallafa

Olivier Giroud ya zama dan wasa mafi shekaru da ya ci wa Faransa kwallo a tarihi bayan nasarar da suka samu a wasansu da Austria.

Da wannan nasarar Faransa ta koma ta biyun karshe a rukunin da take wanda Croatia ke jagoranta.

Les Bleus ne suka mamaye wasan, Kylian Mbappe ne ya fara cin kwallo amma aka hana kwallon saboda an ce an yi satar gida shi kuma Aurelien Tchouameni ya yi wata watsiya ta daki turke ta fita.

Giroud ne ya bai wa Mbappe kwallo ya jefa ta farko, ya yanka yan baya da yawa kafin ya buga kwallon daga wajen yadi na 16.

Dan wasan gaban AC Milan Giroud mai shekara 35 ne ya kara kwallo ta biyu .

Dan wasan me shakara 35 da kwana 357, ya girmi Roger Marche lokacin da ya ci Sifaniya a watan Disambar 1959.

Kwallo biyu ne yanzu ya yi masa saura tsakaninsa da Thierry Henry na Faransa da yake da kwallo 51.

Ba dan nasarar da Faransa ta yi ba da ta zama ta karshe a wannan rukuni, yanzu tana saman Austria da take ta karshe.