Yadda na taimaka wa Safara'u shiga waƙa - Mr 442

An wallafa

Fitaccen matashin mawakin nan na arewacin Najeriya, Mubarak Abdulkarim wanda aka fi sani da 442 ya bayyana alakarsa da Safiya Yusuf wato Safa.

A hirarsa da BBC, 442 ya bayyana cewa ya karfafa wa Safiya gwiwa ne sakamakon mawuyacin halin da ta shiga bayan fitar bidiyon tsiraicinta.