Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real 2-1 Chelsea: An ya Chelsea za ta taka rawar gani a bana?
Kocin Chelsea, Enzo Maresca ya ce yana "kokarin warware" dabi'ar 'yan wasansa da suke bari ana cin ƙungiyar ƙwallaye da yawa.
Real Madrid ta doke Chelsea 2-1 a Charlotte a wasan sada zumunta da suka buga a Amurka, don shirin tunkarar kakar bana.
Dani Ceballos da Brahim Diaz ne suka ci wa Real kwallayen tun kan rabin lokaci, yayin da Noni Madueke ya zare ɗaya.
An zura wa Chelsea kwallo 12 a wasa biyar da ta yi a Amurka, wadda aka ci 4-0 a karawa biyu, ita kuma ta yi nasara ɗaya.
Maresca ya ce ya tattauna da ƴan wasa kan yadda ake zura ƙwallaye da yawa a ragar Chelsea, irin matsala da ta fuskanta kenan a kakar da ta wuce.
Maresca bai yi canji ba a minti 45 ɗin farko a wasan sada zumunta da Real, waɗanda suka je hutu Real ta yi nasara a karawar, duk da damar da Christopher Nkunku ya samu.
Har yanzu dai ƙungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama na buga wasannin ba tare da fitattun ƴan ƙwallonta ba, amma dai Vinicius Jr na ci gaba da taka rawar gani.
A makon nan Jude Bellingham da Kylian Mbapppe za su koma Real Madrid, bayan da suka yi hutu, saboda gasar Euro 2024 da suka buga.
A ranar Lahadi Chelsea za ta kara da Inter Milan a wasan sada zumunta na karshe a Stamford Bridge, kafin wasan farko a gasar Premier a gida da Manchester City ranar 18 ga watan Agusta.
A ranar Laraba 14 ga watan Agusta ne Madrid za ta kara da Atalanta a gasar Uefa Super Cup da za a yi a birnin Warsaw, wanda ake fafatawa tsakanin masu rike da Champions League da mai Europa League, a matsayin labulen buɗe gasar Turai.