Me ya kamata a yi a ranar sabuwar shekarar Musulunci?

An wallafa

Yau ne ɗaya ga watan Muharram, shekarar 1445 bayan hijira. Ita ce rana ta farko a kalandar Musulunci.

An fara amfani da watannin Musulunci ne bayan hijirar Annabi Muhammad (SAW) daga Makka zuwa Madina.

Wannan ne dalilin da ya sa ake rubuta ta 1445 A.H, ma'anar 'A' din na nufin bayan hijira, yayin da 'H' din ke nufin hijira.

Ba wani watan da za a ce ga iyakar kwanakin sa kamar yadda yake a shekarar Turawa, kasancewar ganin wata ne ke tantance kwanakin kowane wata.

Yawanci akan samu bambancin kwanaki 11 tsakanin shekarar Musulunci da ta Turawa, yayin da ta Musulunci ke da mafi arancin kwanaki.

Musulmi na murnar sabuwar shekarar ne saboda tunawa da hijirar da Annabi Muhammad (SAW), daga Makka zuwa Madina.

Hakan yana da mahimmanci a Musulunci saboda yana taimaka wa Musulunci wajen ƙara fahimtar asalin inda aka samo shekarar da kuma yadda Musulmai suka zama tsintsiya ɗaya.

Sheikh Abdulsalm Babangwale wani malamin Addini ne a Najeriya ya kuma ce sabuwar shekarar musuluncin rana ce da kjowanne musulmi ya kamata ya yi muran ya kuma bugi kirji da ita, kasancewar da shekarar nan Annabi ya yi hijira ya kuma kafa daular Muluncin a Madina.

Ya kara da da cewa ba abin da sunna ta koyar game da murna a shekarar musulunci shi ne na idin karama da babbar sallah, sai kuma idin Juma'a da ke maimaituwa a kowanne mako.

''Dan haka babu wani biki na musamman da shari'a ta ware, wanda idan an yi shi za a samu lada''

Sheikh Babangwale ya ce babu wani biki da ake yi na musamman wanda za a sanya sabbin tufafi ko sauya abinci na musamman ko gaishe-gaishe domin wannan ranar ba.

''Amma duk da haka abin da ya kamata mutum ya yi shi ne ya sanya a ransa cewa yau ne sabuwar shekarar musulunci, kuma ya zage dantse domin kara himma wajen aikata ayyukan alheri, kuma idan yana aikata wasu kura-kurai ya tuba ya daina''.

Haka kuma ana so Musulmi su riƙa tunawa da gwagwarmayar da Annabi Muhammad (SAW) da Sahabbansa suka sha kafin Musulunci ya samu tsayuwa da ƙafafunsa.

Haka kuma ana shawartar Musulmi da su riƙa azumtar ranar ɗaya ga watan Muharram da kuma addu'o'i a kowace shekara.

Jerin watannin shekarar Musulunci

  • Muharram
  • Safar
  • Rabi al-Awwal
  • Rabi al-Thani
  • Jumada al-Awwal
  • Jumada al-Thani
  • Rajab
  • Sha’ban
  • Ramadan
  • Shawwal
  • Dhul al-Qadah
  • Dhul Hijjah