Bajintar da Bayern ta yi a kan Barca a Champions League

An wallafa

Ranar Talata Bayern Munich ta doke Barcelona da ci 2-0 a wasan na biyu a cikin rukuni a Champions League a Jamus ranar Talata.

Bayern ta fara zura kwallo ta hannun Lucas Hernandez, bayan da suka koma zagaye na biyu daga baya Leroy Sane ya ci na biyu.

Bayern Munich ta yi wasa 30 a cikin rukuni ba tare da rashin nasara ba a Gasar Zakarun Turai.

Real Madrid ce mai wannan bajintar tsakanin 2012 zuwa 2017.

Bayern ta ci wasa 27 da yin canjaras uku kenan a fafatawar cikin rukuni, ta kuma yi nasara a wasa tara a jere har da bakwai daga ciki da kwallo bai shiga ragarta ba.

Bayern ta ci wasa biyu a jere a bana, karo na 14 da take wannan kwazon a Gasar Zakarun Turai.

Wannan shi ne karo na 14 da aka fafata tsakanin Bayern Munich da Barcelona a wasannin Zakarun Turai.

Kungiyar Jamus ta yi nasara a karo na 10, yayin da ta Sifaniya ta ci biyu da canjaras biyu.

Ranar 7 ga watan Satumba Barcelona ta dura 5-1 a ragar Victoria Polzen a Camp Nou, ita kuwa Bayern ta je ta ci Inter Milan 2-0 a wasan farko a cikin rukuni a Champions League.