Man United za ta kara da Arsenal a Amurka

US Tour 2024

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United da Arsenal za su fafata a Amurka ranar Lahadi a wasan sada zumunta domin shirin tunkarar kakar 2024.

Wasa na uku da United za ta kara kenan, bayan rashin nasara a hannun Rosenborg 1-0, sannan ta doke Rangers 2-0.

Itama Arsenal wasa na uku kenan za ta fafata, bayan da ta doke Leyton Orient 2-0 da kuma tashi 1-1 da Bournemouth

Wasannin da Man United ta buga da waɗanda ke gabanta

  • 15 ga watan Yuli: Man Utd 0-1 Rosenborg
  • 20 ga watan Yuli: Man Utd 2-0 Rangers
  • 28 ga watan Yuli: Man Utd da Arsenal - SoFi Stadium, Los Angeles
  • 1 ga watan Yuli: Man Utd da Real Betis - Snapdragon Stadium, San Diego
  • 4 ga watan Agusta: Man Utd da Liverpool - Brice Stadium, South Carolina
  • 10 ga watan Agusta: Community Shield: Man City da Man Utd - Wembley

Wasannin da Arsenal ta buga da waɗanda ke gabanta

  • 20 ga watan Yuli: Arsenal 2-0 Leyton Orient
  • 25 ga watan Yuli: Arsenal 1-1 Bournemouth
  • 28 ga watan Yuli: Arsenal da Man Utd - SoFi Stadium, Los Angeles
  • 1 ga watan Agusta: Arsenal da Liverpool - Lincoln Financial Field, Philadelphia
  • 7 ga watan Agusta: Arsenal da Bayer Leverkusen, Emirates Stadium
  • 11 ga watan Agusta: Arsenal da Lyon, Emirates Stadium

Ƴan wasan Arsenal da aka je da su Amurka

Masu tsare raga: Karl Hein, Tommy Setford, Lucas Nygaard, Alexei Rojas

Masu tsare baya: Ben White, Oleksandr Zinchenko, Jurrien Timber, Josh Nichols, Gabriel, Jakub Kiwior, Ayden Heaven, Omar Rekik

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Masu buga tsakiya: Thomas Partey, Jorginho, Michal Rosiak, Myles Lewis-Skelly, Martin Odegaard, Emile Smith Rowe, Fabio Vieira, Ethan Nwaneri, Salah–Eddine Oulad M’Hand, Jimi Gower

Masu cin ƙwallaye: Leandro Trossard, Gabriel Martinelli, Reiss Nelson, Charles Sagoe Jr, Gabriel Jesus, Kai Havertz, Eddie Nketiah

Haɗuwa a baya bayan nan da aka yi tsakanin Man United da Arsenal

Arsenal ta doke Manchester United gida da waje a Premier League a kakar da ta wuce, inda ta ci 3-1 a Old Trafford, sannan ta yi nasara 1-0 a Emirates.

A kakar 2023 da suka haɗu a Amurka a wasan atisaye, United ce ta ci 2-0 ta hannun Bruno Fernandes da Jadon Sancho cikin watan Yuli a MetLife Stadium a New Jersey.

Filin wasa na SoFi da ke Los Angeles

An buɗe filin wasa na SoFi a 2020, wanda ke karbar bakuncin wasannin ƙwallon zari ruga, inda Los Angeles Rams da Los Angeles Chargers ke amfani da shi.

Filin kan ɗauki ƴan kallo 70,000, yana daga cikin inda za a kara a gasar kofin duniya a 2026 da gasar Olympic ta 2028.