Mutum 30 sun mutu a turmutsitin bikin bauta a Indiya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Hukumomi a Indiya sun tabbatar da mutuwar aƙalla mutum 30 tare da jikkatar fiye da 60 a wani turmutsitsin bikin addinin Hindu a ƙasar.

Turmutsitsin ya auku ne tsakanin ƙarfe 1:00 zuwa 2:00 na daren ranar Laraba, a lokacin da wani gungun masu ziyarar ibada suka karya shingen da masu ziyarar ke tsayuwa kafin su yi wanka a kududdufi ''mai tsarki''.

Bikin Kumbh Mela, da ake gudanarwa bayan kowace shekara 12 ya kasance babban taron addinin Hindu a faɗin duniya.

Taron bikin - wanda aka kwashe fiye da mako shida ana yi, ya ɗauki hankalin miliyoyin mutanen duniya.

Masu ibadar sun yi imanin cewa wanka a kogin kan wanke zunubi tare da samun yafiya.

Cikin wata sanarwa da gwamnatin ƙasar ta fitar, ta ce adadin mutanen da suka mutu ya kai 30, yayin da wasu 60 suka jikkata.

An ga jami'an bayar da agajin gaggawa suna kwashe gawarwaki a kan gadajen ɗaukar maras lafiya.

Firaminista Narendra Modi da ministocin tarayya ciki har da Ministan harkokin cikin gida Amit Shah sun yi ta'aziyya ga waɗanda suka mutu sakamakon turmutsistin.

Sai dai gwamnatin Uttar Pradesh ƙarƙashin jam'iyyar Bharatiya Janata Party (BJP) Yogi Adityanath, ta yi shiru kan adadin waɗanda suka mutu.

Duk da da wannan turmutsitsi, wasu masu ibadar sun ce za su ci gaba da bikin ibadar domin ci gaba da wanka a kududdufin.

Aƙalla mutum miliyan 50 ne suka yi wanka a kududdufin a yau Laraba, inda kawo yanzu waɗanda suka yi wanka a kududdufin ya kai mutum miliyan 249.8 tun farkon fara bikin.