'Gazawarmu ce ta jefa matasan Najeriya halin da suke ciki'

'Gazawarmu ce ta jefa matasan Najeriya halin da suke ciki'
An wallafa

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamiso ya ce gazawar shugabanci da Najeriya ta fuskanta a shekarun baya, ta fuskar samar da ingantaccen ilmi da tarbiyya ga yara na iya zama sanadin taɓarɓarewar tsaron da ya addabi ƙasar kamar Boko Haram da 'yan fashin daji.

Alhaji Sule Lamiɗo ya bayyana hakan ne yayin zantawa da BBC a wani ɓangare na hirarraki da wasu jiga-jigan siyasar ƙasar kan cikar mulkin dimokraɗiyya shekara 25 da kafuwa a Najeriya.

Jigo a jam'iyyar hamayya ta PDP ya kuma yi nuni da cewa akasarin matasan da ke cikin harkar Boko Haram da 'yan fashin daji, sun taso ne a shekarun da shugabanni kamarsa suka yi wasarairai da batun samar da ingantaccen ilmi da gina tarbiyya da ɗa'a, lamarin da ya ce ya haifar da wannan matsala.