Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaɓen Iran: Waye zai zama sabon shugaban ƙasa, wane sauyi za a samu?
A ranar 28 ga watan Yuni ne Iran za ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa. Za a yi zaɓen ne shekara guda kafin lokacin da ya kamata a gudanar da shi, saboda mutuwar shugaban ƙasar Ebrahim Raisi a wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu a watan Mayun da ya gabata.
A matsayinsa na malami mai tsattsauran ra'ayin Islama, kuma makusancin jagoran addini na ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei, Raisi ya ƙarfafa ikon irin na masu ra'ayin mazan jiya a faɗin jamhuriyyar musuluncin.
Kundin tsarin mulkin ƙasar ya ce dole a zaɓi sabon shugaban ƙasa kwana 50 bayan mutuwar wanda ke mulki, wanda hakan ya bai wa jam'iyyu lokaci ƙalilan na sanar da ƴan takararsu.
Duka manyan ƴan takarar masu ra'ayin mazan jiyan sun fito ne daga ɓangarorin jam'iyyar da ta rarrabu.
Sai dai bayan rashin cancanta sosai a zaɓen ƴan majalisar da aka yi tun da fari, da kuma kama masu zanga-zangar da aka dinga yi a baya-bayan nan, da dama daga cikin ƙungiyoyin da ke son kawo sauyi da ɗaiɗaikun mutane sun sanar da ƙaurace wa zaɓen.
Su wane ne ƴan takara?
Masu sanya ido na kallon zaɓen na Iran a matsayin wanda babu sakin mara kuma babu gasa a cikinsa kasancewar tasirin manyan hukumomi wajen zaɓen ɗan takara.
Majalisar magabata - wadda ke taka muhimmiyar rawa a siyasar ƙasar, wajen tantance ƴan takarar ƴan majalisar dokoki, da na shugaban ƙasa da majalisar ƙwararru - ta amince da ƴan takara shida a cikin 80 da suka yi rajistar tsayawa takara.
1. Mohammad Bagher Ghalibaf: Mai shekara 62, ya taɓa zama kakakin majalisar dokokin ƙasar na tsawon shekara huɗu da suka wuce.
Kuma ya tsaya takarar shugabancin ƙasar sau uku, inda ya sha kaye sau biyu.
Ya janye wa Raisi a shekarar 2021, sannan yana da tarihin riƙe manyan muƙaman soji kuma shi ne ya fi kowa daɗewa a matsayin magajin garin babban birnin ƙasar, Tehran na shekara 12.
2. Amirhossein Ghazizadeh Hashemi: Mai shekara 53, likitan tiyatan kunne da hanci da maƙogwaro ne.
Mutum ne mai ra'ayin ƴan mazan jiya. Ya zama ɗan majalisa, har na tsawon wa'adi huɗu.
A baya-bayan nan ya riƙe muƙamin mataimaki na musamman ga shugaba Raisi.
Ya tsaya takarar shugaban ƙasa a shekarar 2021 inda ya zo na huɗu da ƙuri'a ƙasa da miliyan ɗaya- a fafatawar da kai ga samun kusan ƙuri'u miliyan huɗu da suka lalace a zaɓen.
3. Saeed Jalili: Mai shekara 58, wakili ne a majalisar da ke shiga tsakanin majalisar magabata da ta dokokin ƙasar.
Kuma shi ya jagoranci tawagar tattaunawa kan nukiliya na shekara huɗu.
Ya tsaya takarar shugabanci ƙasar sau biyu, inda ya janye wa Ebrahim Raisi a zaɓen shekarar 2021.
4. Masoud Pezeshkian: Mai shekara 70, ƙwararran likitan tiyatar zuciya ne.
Ya zama ɗan majalisa na tsawon wa'adi biyar, ya riƙe muƙamin ministan lafiya na shekara huɗu.
Ya yi suna wajen faɗin abin da ke ransa gatsai, ya fito fili ya yi suka ga yanayin siyasa da matsalar cin hanci da rashawa a ƙasar.
Ya fito fili ya dasa ayar tambaya kan yadda gwamnati ta yi kan batun mutuwar Mahsa Amini a lokacin a take tsare a hannun ƴan sanda.
Shi kaɗai ake yi wa kallon ɗan takarar da ke bangaren da ke son kawo sauyi a cikin ƴantakarar shugaban ƙasar, lamarin da yasa wasu ke kallonsa a matsayin shugaban da zai kawo ci-gaban ƙasa sosai.
5. Mostafa Pourmohammadi: mai shekara 65, shi kaɗai ne malamin addini a cikin ƴan takarar shida da majalisar magabatan ta amince da su.
Ɗansiyasa ne mai ra'ain ƴan mazan jiya, wanda aka fi sani kan rawar da ya taka a kwamitin da ake cewa 'kwamitin mutuwa,' wadda ta kai ga kashe fursunonin siyasa a shekarar 1988, kwamitin da marigayi Raisi ya kasance wakili.
6. Alireza Zakani: Mai shekara 59, ya kasance magajin garin Tehran a tsawon shekara ukun da suka wuce.
Ɗan siyasa ne mai ra'ayin ƴan mazan jiya ya shiga siyasa ne ta Basij, wani reshe na dakarun juyin-juya-halin na ƙasar.
Kuma ya zama ɗan majalisa na tsawon wa'adi huɗu.
Shin ana barin mata su tsaya takara?
A tsawon kwana biyar da aka ware domin rajistar ƴan takara, mata huɗu ne suka bayyana muradin shiga takarar shugabancin ƙasar.
A karon farko biyu daga cikinsu sun fito ne daga ɓangaren masu ra'ayin ƴan mazan jiya, ɗaya ta fito daga masu neman kawo sauyi, ta huɗunsu kuma ta yi rajista a matsayin mai zaman kanta.
Matan sun yi rajista ne duk da cewa a ƙarƙashin kudin tsarin mulkin ƙasar ya ce ana zaɓen shugaban ƙasa ne daga cikin maza ƴan siyasa da masu addini.
Babu wata matar da aka taɓa amincewa ta tsaya takara a zaɓen shugaban ƙasa 13 da aka yi tun lokacin kafuwar jamhuriyyar Islamar.
Sai dai wasu masu fafutukar kare haƙƙin mata na ja da hakan.
Shin sabon shugaban ƙasar zai kawo sauyi?
Bisa la'aki da yadda abubuwa ke tafiya, shugaban ƙasa a shi ne ke yanke hukunci kan manufofin gwamnati ba.
Jagoran addini da kuma manyan hukumomin da ke ƙarƙashinsa ke da ƙarfin iko.
Don haka akwai yiwuwar babu wani gagarumin sauyi da za a gani a manufofi ƙasar na cikin gida da kuma na wajen ƙasar ba tare da Ayatollah Khamenei ya ce a yi hakan ba.
Masu sanya ido da dama sun yi amanna cewa sauyi kan batun shirin nukiliyar ƙasar da amicewa da Isra'ila a matsayin ƙasa ba abu ne da wani sabon shugaban ƙasa zai iya yi shi kaɗai ba.
Waye zai zaɓi sabon jagoran addini?
To ko makomar Iran ta dogara ne kan sabon shugaban ƙasa?
Ayatollah Khamenei a yanzu shekararsa 85, don haka tambaya kan wanda zai gaje shi na ci gaba da ƙaruwa.
A cewar kundin tsarin mulki, majalisar ƙwararru ce ke da alhakin zaɓen sabon jagoran addini.
Duk da haka, aƙalla a hukumance shugaban ƙasa ba shi da wata rawar da zai taka wurin zaɓen wanda zai gaji jagoran addinin.
Idan aka samu tashin hankali bayan mutuwar jagoran addini, shugaban ƙasa na da dama fiye da ɗaya na yin tasiri kan wanda zai zamo sabon jagoran addinin.
Sai dai a bayyane take cewa a tsawon shekara 40, shugaban ƙasa bai taɓa samun aiwatar da duka nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora masa ba.
"Ayatollah Khamenei na juya ragamar shugabancin ƙasar a tsawon shekara 35 da suka wuce, ta yadda ko da ya mutu, kuma ko ma waye sabon shugaban ƙasa, tsarin da ya bari zai iya gudanar da al'amuran ƙasar a karan kansa.