Ku San Malamanku tare da Nasir Sheikh Ado Musa

Ku San Malamanku tare da Nasir Sheikh Ado Musa
An wallafa

Shirin Ku San Malamanku na wannan makon ya tattauna ne da matashin malami a birnin Bauchi, Nasir Sheikh Ado Musa.

An dai haifi matashin malamin ne a birnin Bauchi.

Sheikh Nasir ya yi ilimin zamani da na addini inda har ta kai ga ya samu shedar kammala digiri na biyu.

Sheikh Nasir ya ce ya fara karatun addinin Musulunci a wurin mahaifinsa.

Matashin ya ce yana da mata biyu da 'ya'ya biyar.

Matashin malamin ya ce abin da ya fi girgiza shi shi ne lokacin da 'na samu kaina a Raudah wato makwancin Annabi Muhamamd (SAW) sai na ji kamar ba ni ba domin sai na taba jikina sannan na tabbatar ni din ne."

Ku shiga cikin bidiyon domin jin karin bayani daga bakin matashin malamin.