Rasuwar Sarauniya Elizabeth II: Shekarar faɗi tashi

An wallafa

Kawun Elizabeth, Yariman Wales, ya zama sarki a 1936, amma ba shi da ɗa ko ɗaya.

Sai Elizabeth wadda ba ta da yayye maza, ta zama ta biyu a kan layin gadon sarauta.

Amma kawun nata, ya so ya auri wata bazawara ƴar Amurka, Wallis Simpson duk da ƙin amincewar masarautar Birtaniya.

A wannan shekarar ɗan uwansa mahaifin Elizabeth ya zama Sarki George na shida.

Sai kuma Elizabeth tana shekara 10 ta zama mai jiran gadon sarautar.