Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kama mutum 25 bisa zargin yunkurin juyin mulki a Jamus
An kama mutum ashirin da biyar a sassa daban-daban na kasar Jamus bisa zargin yunkurin kifar da gwamnati.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu gungun masu ra'ayin rikau da manyan tsofaffin sojoji sun shirya kai hari a ginin majalisar dokokin kasar, Reichstag, domin su kwace mulki.
Wani dan kasar Jamus da ake kira yarima Heinrich XIII, mai shekara 71, ake zargi da shugabantar masu kitsa kifar da gwamnatin.
A cewar masu shigar da kara na gwamnati, yana daya daga cikin mutum biyu na gungun mutanen da aka kama a jihohi 11 da ke fadin kasar.
Mutanen da suka kitsa juyin mulki sun hada da 'yan kungiyar masu tsattsauran ra'ayin rikau ta Reichsbürger [Citizens of the Reich], wadda 'yan sandan kasar Jamus suka dade suna sanya ido a kanta bisa munanan hare-haren da aka kai a baya da kuma karairayi game da wariyar launin jinsi.
Kazalika sun kin yarda su amince da sabuwar kasar Jamus.
An kiyasta cewa maza da mata kusan 50 ne ake zargi da shiga cikin gungun da ya yi yunkurin kifar da gwamnati domin ya maye gurbinta da wata sabuwar gwamnati irin wadda aka yi a Jamus a 1871 - wato wata daula da aka kira the Second Reich.
"Kawo yanzu ba mu san sunan wannan kungiyar ba," a cewar mai magana da yawun ofishin masu shigar da kara.
An kai samame ne a wurare da dama na kasar kuma an kama mutum biyu a Austria da Italiya, a cewar kamfanin dillancin labaran DPA na kasar Jamus.
Za a yi wa mutanen da aka kama tambayoyi nan gaba a yau.
Ministan Shari'a Marco Buschmann ya wallafa sakon Tuwita da ke cewa an gudanar da gagarumin samame na yaki da ta'addanci kuma ana zargi an "kitsa kai hare-hare a gine-ginen shugabannin gwamnati."