An dage gasar kofin Afirka da aka tsara yi a 2023 a Ivory Coast

An wallafa

Shugaban hukumar kwallon kafar Afirka, Patrice Motsepe ya sanar da dage gasar cin kofin nahiyar Afirka daga 2023 an mayar 2024 a Ivory Coast.

Tun farko an tsara gudanar da gasar tsakanin Yuni zuwa Yulin 2023, sai dai lokacin damuna ne da ake mamakon ruwa a kasar.

Shugaban ya fada a babban birnin Rabat a Morocco cewar, ‘’Ba za muyi kasada ba’‘

Da yake za a buga gasar kofin duniya a Qatar a watan Nuwamba zuwa Disambar shekarar nan, mun yanke shawarar kai wasan zuwa 2024 maimakon dawo da karawar kusa‘‘.

Hakan na nufin cewar a karo biyu a jere za a buga gasar cin kofin nahiyar Afirka tsakanin Janairu zuwa Fabrairu, kamar yadda aka yi a Kamaru a shekarar nan.

A shekarar 2017, Caf ta sanar da cewar za ta mayar da buga wasannin tsakanin Yuni zuwa Yuli, maimakon Janairu zuwa Fabrairu, don kawo karshen takaddama da kungiyoyin Turai.

Kungiyoyin Turai kan hana ‘yan wasan Afirka zuwa buga gasar nahiyar, domin ci gaba da fafatawa a wasanninsu, wanda a lokacin gasa ta dauki dumi.

A lokacin shugabancin, Issa Hayatou bai saurari kungiyoyin Turai kan matsin lamba da suke yi na sauya wasannin kofin Afirka da ake yi tsakanin Janairu zuwa Fabrairu ba.