Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man Utd ta yi wa Saudiyya gwanjon Sancho da Antony, West Ham na dab da aron Antony
Manchester United ta gabatar wa ƙungiyoyin Saudiyya ƴan wasanta na gaba na gefe Jadon Sancho, na Ingila da kuma takwaransa na Brazil Antony, inda take buƙatar kusan fam miliyan 50 a kan kowanne. (Evening Standard)
West Ham ta kusa cimma yarjejeniyar karɓar aron Kalvin Phillips daga Manchester City amma kuma duk da haka Juventus ka iya shan kanta a kan ɗan wasan na tsakiya na Ingila. (Mail)
Ɗan wasan gaba na Ajax da Netherlands Brian Brobbey, mai shekara 21, zai so tafiya Manchester United domin kasancewa tare da tsohon kociyansa Erik ten Hag. (Football Insider)
Chelsea ba ta da niyyar sayar da ɗan bayanta Levi Colwill, ɗan Ingila mai shekara 20, a watan nan duk da buƙatarsa da Liverpool ke yi. (Teamtalk)
Newcastle na neman Bayern Munich ta biya ta kusan fam miliyan 12 a kan ɗan bayanta na Ingila Kieran Trippier, wanda ke son tafiya Jamus. (Sky Germany daga Sky Sports)
haka kuma ƙila a shawo kan Newcastle ɗin ta sayar da ɗan gabanta na gefe na tawahar Paraguay Miguel Almiron, wanda Al-Shabab ta Saudiyya ke so. (Guardian)
Newcastle ɗin na ganin Morgan Gibbs-White, mai shekara 23, a matsayin wanda ya dace ya maye gurbin Almiron to amma kuma ba lalle ba ne ƙungiyarsa Nottingham Forest ta yarda ta rabu da gwanin matashin ɗan wasa nata mai. (Telegraph)
An gaya wa Chelsea da Manchester United cewa Nice ba za ta saurari buƙatarsu ta neman sayen ɗan wasanta na baya ba na tawagar Faransa Jean-Clair Todibo, a wannan watan na Janairu ba. (90 Min)
Bisa ga dukkan alamu fatan West Ham na sayen Armando Broja, mai shekara 22, a watan nan na Janairu, ba zai tabbata ba saboda Chelsea na son aƙalla fam miliyan 50 ne a kan ɗan gaban na Albania. (Football Insider)
Lyon na ƙoƙarin sake ɗauko Karim Benzema, daga Al-Ittihad, ta Saudiyya, wanda hakan zai sa ya kasance babban ɗan wasa na baya-bayan nan da zai bar gasar ta Saudiyya. (Guardian)
Newcastle ba za ta iya sayen ɗan wasan tsakiya na Brazil ba, Ederson a watan nan kasancewar ƙungiyarsa, Atalanta ta yi masa farashin tsakanin fam miliyan 30 zuwa 40. (Football Insider)
Ƙungiyar Al-Ettifaq ta Saudiyya na sha'awar ɗan wasan tsakiya na Everton da Mali Abdoulaye Doucoure, mai shekara 31. (Guardian)
Shirin bayar da aron ɗan wasan gaba na gefe na Manchester United da Uruguay Facundo Pellistri, mai shekara 22, ga Granada ya ci tura a kan rashin cimma yarjejeniya a kan kason albashin da ƙungiyar ta Sifaniya za ta rinƙa bayarwa na ɗan wasan, inda ita kuma PSV Eindhoven ke jiran tsammani. (Mail)
Burnley na ƙoƙarin cimma yarjejeniyar sayen ɗan bayan Montpellier Maxime Esteve, ɗan Faransa mai shekara 21. (Fabrizio Romano)
AC Milan ta tuntuɓi tsohon ɗan wasan tawagar Ingila ta matasa Tosin Adarabioyo, mai shekara 26, kasancewar kwantiragin ɗan bayan na Fulham zai ƙare a ƙarshen kakar nan. (Sky Sports)