An dakatar da Klopp daga jan ragamar Liverpool wasa daya

An wallafa

An dakatar da Jurgen Klopp daga jan ragamar wasa daya, bayan daukaka kara kan cin tarar da aka yi masa, bayan jan kati a wasa da Manchester City.

Tun farko an ci tarar kociyan Liverpool £30,000, bayan da wani kwamiti mai zaman kansa ya bibiyi wasan da kociyan na nuna hali na rashin da'a.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta sake nazarin abun da ya faru, bayan da kwamitin ya aike mata rahoto a rubuce kan halayar da kocin ya nuna.

Dakatarwar ta fara aiki nan take, za kuma ta fara ranar Asabar a karawar da Liverpool za ta yi da Southampton a gasar Premier League.

An bai wa Klopp jan kati a wasan da Liverpool ta ci City, bayan da ya nufi matakimakin alkalin wasa kamar zai cinye shi danye, bayan da ba a bayar kalubalantar katin gargadi a ketar da ya ce an yi wa Mohamed Salah.

Bayan da aka tashi daga fafatawar kociyan dan kasar Jamus ya nemi afuwa kan halin rashin kyautawa da ya yi.

Saboda haka Klopp zai biya tarar £30,000 da hukuncin dakatarwa karawa daya, an kuma ja kunnensa da kaucewa nuna hali na rashin da'a nan gaba.