Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Benzema ya yaga barakar Barcelona a Copa del Rey
Real Madrid ta kai wasan karshe a Copa del Rey, bayan da ta doke Barcelona 4-0 a wasa na biyu ranar Laraba a Nou Camp.
Daf da za su je hutu Vinicius Junior ya ci wa Real kwallon farko, Karim Benzema ya kara na biyu minti biyar da komawa zagaye na biyu.
Tsohon dan wasan tawagar Faransa shine ya ci na uku, kuma na biyu a wasan hamayya na El Clasico a bugun fenariti.
Daf da za a tashi kenan Benzema ya kara na uku na hudu a wasan, karo na biyu a jere yana cin uku rigis a Real Madrid.
A karshen mako Real ta caskara Valladolid 6-0, inda Benzema ya ci uku rigis a karon farko a bana a Real Madrid.
Real Madrid ta kai zagayen gaba da cin kwallo 4-1 gida da waje, bayan da Barcelona ta yi nasarar cin 1-0 a wasan farko ranar 2 ga watan Maris.
Wasa na biyar kenan da aka kara tsakanin manyan kungiyoyin Sifaniya, Barcalena ta yi nasara a uku, Real Madrid ta ci biyu.
Wasa biyar da aka buga a bana tsakanin Barcelon da Real Madrid:
Copa del Rel Laraba 5 ga watan Afirilun 2023
- Barcelona 0 - 4 Real Madrid
La Liga Lahadi 19 ga watan Maris 2023
- Barcelona 2 - 1 Real Madrid
Copa del Rey Alhamis 2 ga watan Maris 2023
- Real Madrid 0 - 1 Barcelona
Sifanish Super Cup Lahadi 15 ga watan Janairun 2023
- Real Madrid 1 - 3 Barcelona
La Liga Lahadi 16 ga watan Oktoban 2022
- Real Madrid 3 - 1 Barcelona
Real Madrid za ta buga wasan karshe a Copa del Rey da Osasuna ranar Asabar 6 ga watan Mayu.
Osauna ta kai wasan karshe da cin Athletic Bilbao 2-1 gida da waje, bayan da suka tashi 1-1 a wasa na biyu ranar Talata, a fafatawar farko Osasuna ta ci 1-0.
Karon farko da Osasuna za ta buga wasan karshe a Copa del Rey tun bayan 2005.
Real Betis ce mai rike da Copa del Rey na bara, Real Madrid tana da shi 19, Barcelona ce kan gaba a yawan daukar kofin mai 31 jimilla.
Barcelona ce ta daya a kan teburin La Liga da tazarar maki 12 tsakaninta da Real Madrid ta biyu.
Ranar Asabar 8 ga watan Afirilu, Real Madrid za ta karbi bakuncin Villareal a wasan La Liga, kwana hudu tsakani ta kece raini da Chelsea a quarter finals a Champions League a Sifaniya.
Ranar Litinin 10 ga watan Afirilu Barcelona za ta kece raini da Girona a La Liga a Nou Camp.