Ku San Malamanku tare da Sheikh Abbas Hussain

Ku San Malamanku tare da Sheikh Abbas Hussain
An wallafa

Ku San Malamanku ya tattauna da Sheikh Abbas Hussein, wani malamin addinin musulunci a Najeriya.

An haifi malamin a karamar hukumar Dala da ke jihar Kano kuma ya yi karatun zaure da na Islamiyya.

A cewarsa, ya tashi cikin harkar karatun addini kasancewar kakansu ya assasa wata makarantar allow adda mahaifinsu ke rike da ita.

Ya ce a makarantar ne ya sauke karatun Al-Qur’ani kuma ya yi karatu a hannun malamai da dama ciki har da Sheikh Shariff Zakariyya.