Yadda manoma tattasai suka tafka asara bayan amfani da gurbataccen taki

An wallafa

Manoman tattasai a wasu yankunan arewacin Najeriya na ci gaba da juyayin irin asarar da suka tafka, bayan amfani da suka yi da gurbatattacen takin zamani.

Manoma da dama daga jihar Kano, sun ce sun zuba makudan kudade a noman tattasai na bana, amma ba su samu ko sisi ba, kasancewar ya lalace.

Wakilin BBC da ya ziyarci wasu gonakin tattasai a karamar hukumar Wudil da ke jihar Kano, ya samu manoma na ban ruwa a gonar Masara da Tumatur da Tattasai, sun yi kore shar gwamanin ban sha'awa, sai dai yawanci tattasan sun bushe, wasu kuma sun yankwane.

Malam Ali da ya jima a harkar noman Tattasai da kayan lambu, ya shaidawa BBC sun tafka asara mai tarin yawa a noman tattasai: ''Sai dai ko noman masara watakil a samu wani abun. Ka ga anan gonata na zuba kusan 500,00 amma babu ko na dubu 100 anan, komai ya lalace.

"Takin da muka zuba shi ya haddasa hakan tun lokacin da na zuba shi kenan, amma wanna da babu asarar nan ai sai an samu miliyan daya akai.

An dora alhakin hakan na takin zamani, saboda kafin a zuba takin komai lafiya amma ana zuba takin komai ya sauya, ka ga dai yadda ya yankwane wani ma ya bushe.''

Wani manomin mai suna Malam Awwali da ke kusa da ginar Malam Ali ya ce shi tattasai ya fi son yanayi guda ko dai zafi ko sanyi, amma wannan karon da aka yi yanayin iri biyu a lokaci guda, shi ma ya kara haddasa wannan matsalar. Tattasai ya bushe babu komai.

Yanayin da aka shiga na rashin kyawun yabanya a noman tattasan, ta janyo karancinsa a kasuwanni, kamar yadda wakilin BBC ya gani a ziyarar da ya kai kasuwar 'Yan kaba da ta yi fice wajen saida kayan lambu da gwari a jihar Kano.

Kuma sakataren kungiyar masu saida kayan gwari na jihar Kano Aliyu Muhammadu Bello ya shaida masa cewa tattasai ya yi tsada ana saida buhun shi akan naira 22000 amma a bara ake saidawa kan naira 6000.

Kungiyar dilalan takin zamani ta jihar Kano ba ta ce uffan kan tuntubar da BBC ta yi kan batun gurbataccen takin da ake zargin shi ya lalata amfanin noman tattasan ba, amma hakarmu ba ta cimma ruwa ba.

Amma a baya jami'an tsaro sun yi kamen gurbataccen takin zamanin da ake fargabar ya riga ya shiga hannun manoma.