Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man United za ta ɗauki Ugarte daga PSG kan £42.29m
Manchester United ta amince za ta biya £42.29m ga Paris St-Germain, domin sayen ɗan wasan tawagar Uruguay, Manuel Ugarte.
Cikin ƙunshin yarjejeniyar har da £8.46m karin tsarabe-tsarabe da za a bai wa ɗan wasan da zarar an kammala cinikin.
Ana sa ran Ugarte zai je Manchester United ranar Talata, domin a auna koshin lafiyarsa.
Wannan cinikin ya zo ne a lokacin da Scott McTominay zai koma taka leda a Napoli kan £25.37m.
An daɗe ana ta alakanta Ugarte da United a bana, yanzu zai koma Old Trafford kaka ɗaya tsakani da ya taka leda a PSG, bayan da ya koma can daga Sporting Lisbon.
Mai shekara 23 ya buga wa PSG karawa 37 har da 25 a Lik a bara da ƙungiyar Luis Enrigue ta lashe Ligue 1 na 12 jimilla.
To sai dai United za ta kammala cinikin Ugarte idan ta sayar da McTominay ga Napoli, amma ana da tabbacin cinikin zai faɗa.
Ana sa ran McTominay zai je Italiya a auna koshin lafiyarsa ranar Talata daga baya ya saka hannu kan ƙunshin yarjejeniya.
Idan har Ugarte ya kammala komawa United, zai zama na shida da ta ɗauka a bana, jimilla ta kashe £190m.
United ta sayi ƴan wasa kan £600m tun bayan da ta ɗauki Ten Hag daga 2022.