Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal ta sa Liverpool za ta ci gaba da jira kafin lashe Premier
Ƙwallo biyun da Leandro Trossard ya ci sun sa Liverpool za ta ci gaba da jiran ranar da za ta lashe Premier League, bayan da Arsenal ta doke Ipswich 4-0 ranar Lahadi.
Gunners ta fara cin ƙwallo ta hannun Trossard daga baya Gabriel Martinelli ya kara na biyu bayan samun tamaula daga wajen Mikel Merino.
Daga baya aka bai wa Leif Davis jan kati, sakamakon ketar da ya yi wa Bukayo Saka, hakan ya sa Ipswich ta karasa karawar da ƴan wasa 10 a cikin fili.
Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Trossard ya kara ƙwallo a raga na biyu a wasan, sai Ethan Nwaneri da ya ci wa Gunners na huɗu.
Liverpool za ta buga wasa da Leicester City a King Power ranar Lahadi.
Manchester United, wadda ta sa ƙwazo ta fitar da Lyon a Europa League, ta yi rashin nasara a hannun Wolverhampton 1-0 a Old Trafford.
Ranar Alhamis ne United ta yi namijin kokari wajen yin waje da Lyon, wadda ta ci ƙwallaye daga baya aka farkesu a gasar ta Europa League.
Wolves ta ci ƙwallo daga bugun tazara ta hannun Pablo Sarabia, kuma karo na biyar da ƙungiyar Molineux ta lashe wasa a Premier ta samu maki 38 irin na United.
Chelsea kuwa ta ta doke Fulham 2-1 a wasan hamayya a Craven Cottage, duk da ita aka fara ci daga baya ta farke sannan ta kara na biyu.
Fulham ce ta fara cin ƙwallo a minti na 20 da take leda ta hannun Alex Iwobi, sai dai minti bakwai tsakani Chelsea ta farke ta hannun Tyrique George.
Ana shirin tashi ne Pedro Neto ya ci wa Chelsea na biyu da ya sa ta samu maki ukun da take bukata a wasan na Premier League.