Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amorim ya kasa doke Guardiola karo na uku a jere
Ranar Lahadi aka tashi wasa tsakanin Manchester United da Manchester City 0-0 a karawar mako na 31 a Premier League a Old Trafford.
Karo na 196 da suka kece raini a tsakaninsu kenan, inda City ta buga karawar da fatan samun gurbin Champions League a badi, wadda take ta biyar a teburin Premier.
Ita kuwa Manchester United, tana fatan lashe Europa League na bana, domin ta sake shiga gasar zakarun Turai a baɗi, wadda take ta 13 a teburin Premier.
A wasan na ranar Lahadi, Rubin Amorim ya yi fatan ya doke Pep Guardiola karo na uku a jere amma sai hakan bai samu ba.
Tun bayan da Amorim ya maye gurbin Erik ten Hag a United, ya yi nasara a kan Guardiola cikin Disamba a Etihad da cin 2-1.
Kafin nan ya yi nasara 4-1 a kan Guardiola a wasan karshe a Lisbon a Champions League a kan kociyan Sifaniya.
Waɗanda suka yi nasara uku a jere a kan Guardiola a baya sun haɗa da Jurgen Klopp da kuma Thomas Tuchel.
Ranar Alhamis United za ta fafata da Lyon a wasan zagayen farko a Europa League a Faransa, sannan na biyu wasa na biyu mako makon gaba.