Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Golan Liverpool Alisson zai yi jinyar wata ɗaya
Ana sa ran mai tsaron ragar Liverpool, Alisson zai yi jinya har zuwa tsakiyar watan Nuwamba, sakamakon raunin da ya ji.
Ɗan wasan tawagar Brazil ya ji rauni a wasan da Liverpool ta ci Crystal Palace 1-0 ranar Asabar a Premier League, inda Vitezslav Jaros ya canje shi a minti na 79.
Liverpool tana sa ran Alisson zai koma fagen daga tsakanin 11 zuwa 19 ga watan Nuwamba.
Liverpool za ta kara da Chelsea da Arsenal da Brighton da Aston Villa da RB Leipzig da Bayer Leverkusen a Champions League da Brighton a Carabao Cup ba tare da Alisson ba.
Caoimhin Kelleher ne ya kamata ya tsare ragar Liverpool a karawa da Palace to amma bai da lafiya, shi ya sa aka sa Jaros.
Kelleher, ya tsare ragar Liverpool a League Cup da ta doke Bournemouth da kuma West Ham United.
A cikin Nuwamba wato 24 ga watan, Liverpool za ta fafata da Southampton a Premier League, sannan Real Madrid a Champions League.
Daga nan za ta kara a wasa mai zafi na hamayya a Premier League da Manchester City da Newcastle United da kuma na Mersyside Derby da Everton.