Golan Belgium Casteels ya bar tawagar saboda Courtois zai koma tsare raga

Asalin hoton, Getty Images
Mai tsare ragar Belgium, Koen Casteels ya bar tawagar saboda ya nuna bacin rai sakamakon da Thibaut Courtois zai sake komawa golan kasar.
Casteels shi ne yake tsare ragar Belgium wata 18 da ta gabata, bayan da Courtois ya ce ba zai yi aiki karkashin koci, Domenico Tedesco ba.
To sai dai a watan Janairu hukumar kwallon kafar ta Belgium ta naɗa Rudi Garcia sabon koci, inda Courtois ya ce a shirye yake ya sake komawa buga wa kasar wasanni.
''Abin mamaki ne da hukumar ƙwallon kafa ta Belgium ta buɗe hannu ta karɓi Courtois,'' kamar yadda Casteels ya sanar.
Courtois ya ƙi buga wasa karkashin Tedesco, bayan rashin jituwa da suka samu kan mukamin kƴaftin ɗin tawagar a tsakiyar shekarar 2023.
Daga lokacin Casteel ya fara tsare ragar Belgium har ma a gasar cin kofin nahiyar Turai da aka yi a 2024, inda aka yi waje da kasar a zagayen ƴan 16.
Casteels, wanda ya taka leda a gasar Bundesliga yanzu yana Saudi Arabia, ya daɗe yana madadin Courtois.
Courtois, mai shekara 32, wanda ya buga wa Belgium wasa 102, wanda ake cewa shi ne fitatcen mai tsaron raga a duniya, ya gana da Garcia inda ya sanar da shi a shirye yake ya ci gaba da golan kasar.











