'Abin da ya sa muka ce ƴanbindiga na amfani da makaman jami’an tsaro'

Nuhu Ribado

Asalin hoton, Nuhu Ribadu/X

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Yadda gwamnatin Najeriya ta fara fitowa fili tana zargin jami'an tsaron ƙasar da sayar wa ƴanbindiga makamai ya haifar da muhawara a tsakanin ƴan ƙasar, lamarin da masana ɓangaren tsaro suka ce ai sun daɗe da sani.

Babban mai mai wa shugaban ƙasar shawara na musamman kan sha’anin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ne ya bayyana hakan ranar Alhamis Abuja, lokacin bikin ƙona makamai da aka ƙwace daga hannun ƴanbindiga.

An dai kona makaman da aka kwato ga ‘yan bindiga da sauran waɗanda suka lalace da suka haɗa da bindigogi da yawansu ya kai 2,400 a gaban manyan hafsoshin tsaron ƙasar, da manyan jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a ɓangaren tsaron.

Nuhu Ribadu ya ce galibin makaman da aka ƙonan - waɗanda aka ƙwato daga hannun 'yan bindigar - mallakinjami'an tsaron ƙasar ne.

Mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan tsaron ya kuma tabbatar da cewa galibin makaman da ƴan fashi dajin ke amfani da su, suna samunsu ne daga bara-gurbin jami’an tsaro, waɗanda ya ce suna sayar da bindigogin ta haramtacciyar hanya ga ƴan fashin dajin.

Nuhu Ribadu ya ce ''abin takaici ne waɗanda ke yaƙar ayyukan ta’addanci su ɓuge da tallafa wa masu aikata ba daidai ba''.

Sannan ya ce gwmanatin Najeriya za ta ɗauki tsauraran matakan hukunta waɗanda aka samu da laifin safarar makaman zuwa wasu wurare.

Dama dai ƴan ƙasar da dama sun jima suna kokawa tare da nuna damuwarsu kan yadda ƴan bindigar ke samun makaman da a wasu lokuta ma suka zarta na jami'an tsaron ƙasar inganci.

Mai ba shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaron, ya ce ya zama dole a yaƙi waɗannan ɓata-gari, da ma masu ƙera makaman da ke cikin ƙasa da su ke ci gaba da rurruta matsalar ta tsaro. Kazalika, ya bayyana ƙoƙarin gwamnatin Najeriya wajen ci gaba da yaƙar ‘yan bindiga.

Mun jima da sanin haka - Masana

Masana al'amuran da suka shafi tsaro a Najeriya sun ce iƙirarin Nuhu Ribado tabbataccen al'amari ne da babu kokwanto a cikinsa.

Dakta Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Consulting mai nazarin al'amuran tsaro, ya shaida wa BBC cewa dama tuni suka gano haka.

''Tun lokacin da Alhaji Ali Kwara ya fara yin maganar, muka soma zurfafa bincike a 2021, kuma binciken namu ya tabbatar mana da hakan'', in ji Kabiru Adamu.

Masanin ya ƙara da cewa haka kuma sun samu irin waɗannan bayanai daga wasu jami'an tsaron ƙasar.

''Haka a zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari, in ba ka manta ba babban mai bibiya, wato Auditor Genaral, ya fitar da wasu bayanai da shaidun da suka nuna cewa ƴan ta'adda na amfani da makaman jami'an tsaron ƙasar'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa ''lallai bincikenmu ya tabbatar da wannan iƙirari cewa jami'an tsaro na bayar da makamansu ga 'yanta'adda domin amfani da su''.

Me ya kamata gwamnati ta yi?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A cewar Dakta Kabiru Adamu, haƙƙin daƙile bazuwar makamai daga jami’an tsaron da ake zargi zuwa ga ƴan bindiga ya rataya ne a wuyan gwamnati, kuma idan ta yi da gaske to za a iya samun nasara.

Ya ce, "da farko dai ya kamata ita gwamnati ta ɗauki wannan abu da muhimmanci. Waɗanda suke faɗi cewa akwai matsala, ai su ne suke da haƙƙin gyara, bai dace ba a ce suna fitowa suna faɗi ba, ba tare da sun ayyana matakan da za su ɗauka ba na gyara."

A game da hanyoyin da za a gyara, masanin ya ce suna da yawa. "Ya kamata a riƙa tsaurara bin diddigin tarihin waɗanda za a ɗauka aiki, kuma a riƙa yi ta hanyar da ta dace.

Sannan bayan an ɗauki mutum, shi ma yana da kyau a sake binciken.

"Haka ma tsarin ajiye makamai da yadda za ka karɓa makaman da sauransu, zai yi kyau a gyara ta yadda ko mutum yana so ya aikata laifi, zai ji tsoro."

A ƙarshe ya ce a yi amfani da kimiyya, "wato a sanya na'urar bibiya a makamai da ma jami'an tsaron. Sannan a tsaurara matakan bibiyan jami'an tsaron, sannan idan an samu mai matsala a hukunta shi."

Ƙaruwar ayyukan 'yanbinga a Najeriya

A shekarun baya-bayan nan Najeriya na fuskantar ƙaruwar ayyukan 'yanbindiga, kama daga 'yan Boko Haram da suka addabi yankin arewa maso gabashin Najeriya, musamman a shekarun baya da suka zafafa hare-hare a yankin.

Haka ma a yankin kudu maso gabashin ƙasar, ana fama da 'yan ƙungiyar IPOB da suke yawaita kai hare-hare musamman kan jami'an tsaro.

A shekarun baya an ga yadda 'yan IPOB ke ƙaƙaba dokar zaman gida a wasu ranaku, a wani ɓangare na fafutikar da suke yi na ɓallewa daga Najeriya.

Sannan yankin arewa maso yammaci da arewa ta tsakiya da ke fama da ƙaruwar hare-haren 'yan fashin daji masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

Waɗannan 'yanbindiga sun addabi yankunan arewa maso yamma da arewa ta tsakiyar ƙasar, lamarin da ya tilasta wa wasu al'umomin yankin da dama ficewa daga garuruwansu.