Real Madrid na dab da sayen matashin ɗanwasa Lamini Fati

Asalin hoton, Leganes FC
Real Madrid na shirin sayen matashin ɗanwasa Lamini Fati mai shekara 18 daga ƙungiyar Leganes, kamar yadda jaridar AS ta ruwaito.
Rahoton ya ce tuni Real ta ƙulla yarjejeniya da ɗanwasan mai tsaron baya kuma nan gaba kaɗan za a sanar da ɗaukarsa.
Tun da farko jaridar Relevo ta ce Real za ta biya kusan yuro 100,000 kan Fati, a cewar AS.
An haife shi Sifaniya. Mahaifiyarsa 'yar Angola ce, mahaifinsa kuma ɗan ƙasar Guinea-Bissau.
Ana sa ran zai fara wasa a Real da tawagar ƙungiyar matasa wato Real Madrid C, ko kuma tawagar 'yan ƙasa da shekara 19.
Daga baya kuma ana sa ran zai samu damar komawa ƙaramar ƙungiyar Real ta Castilla, wadda tsohon tauraron ɗanwasan gaba Raul Gonzalez ke horarwa wadda ke buga gasar Primera.
Sai dai ba a sa ran zai samu damar shiga babbar ƙungiyar ta Los Blancos nan kusa, duk da yadda masu tsaron bayanta ke fama da raunuka.







