Sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hezbollah

    • Marubuci, Ido Vock
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon da Isra'ila ta fara aiki bayan shafe sama da shekara ɗaya ana gwabza yaƙi.

Ta fara aikin ne da misalin ƙarfe 04:00 na dare (3:00 agogon Najeriya da Nijar), wadda ta kawo ƙarshen hare-hare na ɗan lokaci.

A yammacin Talata ne Isra'ila da Faransa da Amurka suka sanar da ita, inda Shugaba Joe Biden ya ce ana fatan "za ta zama ta dindindin".

Kowane ɓangare ya yi ta kai hari har zuwa 'yan sa'o'i kafin fara aiki da yarjejeniyar.

Awa huɗu kafin fara aikinta Isra'ila ta fitar da umarni ga mazauna wasu yankunan binrin Beirut kuma awa ɗaya kafin haka ta kai hare-hare. Ita ma Hezbollah ta harba jirage marasa matuƙa zuwa Isra'ilar jim kaɗan kafin a tsagaita wutar.

'Yan mintuna kafin a dakatar da faɗa, rundunar sojin Isra'ilar ta gargaɗi mazauna kudancin Lebanon game da "komawa ƙauyukan da ta ba da umarnin ficewa ko kuma zuwa kusa da sojojinta".

Ta ce rundunar za ta faɗi lokacin da take ganin babu matsala za su iya komawa gida.

Duk da haka, an ga gomman ababen hawa na kan hanyar zuwa kudancin bayan yarjejeniyar ta fara aiki.

A ƙarshen watan Satumba ne Isra'ila ta faɗaɗa hare-hare kan Hezbollah tare da ƙaddamar da samame ta ƙasa bayan sun shafe sama da shekara suna musayar wuta a kan iyakar ƙasar da Lebanon.

Wannan yaƙi shi ne mafi muni a Lebanon cikin shekaru masu yawa, inda hare-haren Isra'ila suka kashe sama da mutum 3,8823, a cewar hukumomin ƙasar.

Abubuwan da yarjejeniyar ta ƙunsa

Shugaban Amurka Joe Biden ya faɗa wa manema labarai cewa an tsara yarjejeniyar ce "da zimmar ta zama ta dindindin".

A ƙarƙashin yarjejeniyar, cikin kwana 60 Hezbollah za ta janye dakarunta da makamai daga yankin da ake kira Blue Line - wata iyaka da ba ta hukuma ba tsakanin Isra'ila da Lebanon - da kuma kogin Litani da ke da nisan kilomita 30.

An ƙirƙiri iyakar Blue Line ne a ƙarshen yaƙin da suka gwabza a 2006.

Dakarun sojin gwamnatin Lebanon za su maye gurbin mayaƙan Hezbollah a yankin, sannan su tabbatar babu wasu sauran makamai ko kayayyakin ƙungiyar da za a sake ginawa, a cewar wani babban jami'in Amurka.

Cikin wannan kwana 60 ɗin dai, Isra'ila za ta dinga janye dakaru da fararen hularta da suka rage, in ji Biden, yana mai cewa hakan zai bai wa fararen hula a ɓangarorin biyu damar komawa gidajensu.

"Wannan sanarwar za ta shimfiɗa ƙa'idojin samun zaman lafiya da zai bai wa ƴan ƙasashen biyu damar komawa gidajensu,'' in ji wata sanarwar haɗin gwiwa da ta fito daga gwamnatocin Amurka da Faransa, ƙasashe biyu da za su taimaka wurin tabbatar da tsare-tsaren da ke ƙasa wanda za su aiwatar da ƙudurin Majalisar Dinkin Duniya da aka gabatar a ƙarshen yakin shekarar 2006.

Firaministan Labanon Najib Mikati ya yi maraba da yarjejeniyar, yana mai cewa wani muhimmin mataki ne na maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar tare da bai wa ƴan ƙasar damar komawa gida.

Sai dai kuma ya buƙaci Isra'ila ta "bi ƙa'idojin yarjejeniyar" ta fice daga yankunan da ta mamaye da kuma mutunta ƙudurin Majalisar Dinkin Duniya.

Shi kuwa ministan muhalli na ƙasar Labanon Nasser Yassin, ya shaidawa BBC cewa, ganin yadda ƙungiyar Hezbollah ta ci gaba da kasancewa a matsayin "jam'iyya" a majalisar dokokin ƙasar, a yanzu ƙasarsa na buƙatar mayar da hankali kan maido da tsarin siyasa da sawwaƙa tattaunawa tsakanin "al'ummomi daban-daban".

Sojojin Lebanon 5,000 za su maye gurbin Hezbollah

Ana sa ran rundunar sojin Lebanon za ta aike da dakaru 5,000 zuwa kudancin ƙasar ƙarƙashin yarjejeniyar, a cewar wani jami'in Amurka.

Sai dai har yanzu akwai rashin tabbas kan irin rawar da za su taka wurin tabbatar da an bi ƙa'idojin yarjejeniyar, da kuma ko za su iya tunkarar kungiyar Hezbollah idan bukatar haka ta tashi, wanda hakan zai iya ƙara dagula al'amura a ƙasar da rarrabuwar kawuna ke da yawa.

Har ila yau, sojojin na Lebanon sun ce ba su da abubuwan da ake buƙata- kudi da ma'aikata da kuma kayan aiki - don sauke nauyin aiwatar da na su ɓangaren yarjejeniyar, ko da yake za a iya sawwake masu hakan ta hanyar gudummuwar da wasu ƙasashe kawayen Lebanon za su bayar.

Sai dai da dama daga cikin jami'an ƙasashen yammacin duniya sun ce an raunata ƙungiyar Hezbollah, kuma wannan lokaci ne da gwamnatin ƙasar Labanon za ta sake maido da iko da dukkan yankunan ƙasar.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce Isra'ila ba za ta ɓata lokaci ba wajen kai farmaki idan Hezbollah ta saɓa wani ɓangare na yarjejeniyar da aka cimma.

"Idan ƙungiyar Hezbollah ta saɓa yarjejeniyar kuma ta yi ƙoƙarin sake tattara makamai, za mu kai hari, idan har ta yi yunƙurin sake farfaɗo da cibiyoyin aikata ta'addanci a kusa da kan iyaka, za mu kai hari."

Biden ya ce Isra'ila "tana da ƴancin kare kanta wanda ya yi daidai da dokokin ƙasa da ƙasa".

Wani ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a na gidan talabijin na Isra'ila ya nuna kashi 37% na ƴan ƙasar na goyon bayan yarjejeniyar, kashi 32% na adawa da kuma 31% na cewa ba su wata matsaya kan lamarin.

Netanyahu ya kuma ce kawo ƙarshen faɗa a Labanon, makwabciyar Isra'ila ta gefen arewa, zai bai wa rundiunar IDF damar mayar da hankali kan "barazanar Iran".

Amurka da Faransa za su sanya ido kan aiwatarwa

Yarjejeniyar dai ta na kamanceceniya ne da ƙudurin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1701, wanda ya kawo ƙarshen yaƙin 2006 tsakanin Isra'ila da Hezbollah.

Ƙarƙashin ƙuduri mai lamba 1701, Sojojin ƙasar Lebanon da kuma undunar kiyaye zaman lafiya ta MDD (Unifil) ne kaɗai naka ba su damar kasancewa a yankunan da ke kudu da kogin Litani.

Sai dai ɓangarorin biyu sun ragi juna da keta ƙudurin.

Isra'ila ta ce an ba Hezbollah damar gina manyan ababen more rayuwa a yankin, yayin da Lebanon ta ce laifukan Isra'ila sun haɗa shawagin da jiragen yaƙinta ke yi a yankin.

Babban jami'in na Amurka ya ce a wannan karon, Amurka da Faransa za su shiga cikin tsarin da ake da shi ya tya ƙunshi ɓangarori uku, wanda ya ƙunshi rundunar UnNIFIL da Lebanon da Isra'ila, waɗanda za su sanya ido kan yadda ake aiwatar da ƙa'idojin yarjejeniyar.

"Dakarun sojin Amurka ba za su kasance a yankin ba , amma za mu bayar da tallafin ayyukan soji ga sojojin ƙasar Lebanon, kamar yadda muka yi a baya. tare da haɗin gwiwar sojojin Faransa," in ji jami'in.

Da yake ishara da damuwar da Isra'ila ta bayyana, Biden ya ce: Ba za a bari Hezbollah ta sake kafa kayayyakin ayyukan ta'addanci a kudancin ƙasar Lebanon ba.