Kungiyar Afenifere ta nemi Tinubu ya shawo kan tsadar rayuwa da rashin tsaro

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Kungiyar Yarbawa zalla ta Afenifere ta yi kira ga gwamnatin tarayya da tashi tsaye don ceto Najeriya da al’ummarta daga durkushewa gaba daya.

Kungiyar ta bayyana damuwarta game da barnata da dukiyar kasar a yayin da rayuwar al’ummar Najeriyar ke kara tabarbarewar tun bayan hawa mulkin gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

A cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban kungiyar Oladipo Olaitandan da mataimakin sakatare na kungiyar, Alade Rotimi John suka fitar sun ce ‘halin da ake ciki ya jefa kasar cikin wani yanayi na tsaka mai wuya da rudani’

‘’ Alummar Najeriya na cikin damuwa matuka sakamakon wahalhalun da ake fama da su da yunwa da rashin tsaro da tsaddar rayuwa da rashin aikin yi da kuma hauhawar farashin kayayaki’,’ in ji kungiyar ta Afenifere.

Kungiyar ta ce wadannan matsaloli sun kara ta'azara halin da alummar kasar ke ciki idan aka kwantata da na baya,

Ta nuna damuwa kan irin rikon sakainar kashi da halin ko in kula da rashin hagen nesa da gwamnati Tinubu ke yi dangane da irin illar da ke tattare da manufofin gwamnati.

Game da haka ne kungiyar ta Afenifere ta yi kashedi kan barnatar dukiyar kasa tana mai cewa: ‘’Dala miliyan 300 kwatankwacin naira biliyan 240 da aka cire na sayan jirgin shugaban kasa da kuma karin naira miliyan 150 alamari ne da ba za'a amince da shi ba’’

Kungiyar ta Afenire ta ce naira miliyan 950 kan sayan sabbin mottocin sulke samfurin Cardilac da limousine da kuma SUV a matsayin motocci na musaman ga shuagaban kasa da naira biliyan 21 don yi wa sabon gidan mataimakin shugaban kasa kwaskwarima da kuma naira biliyan 90 a matsayin tallafin kudin aikin adini na sauke farali da kuma naira biliyan 10 don yi wa gidan shugaban kasa a Lagos kwaskwarima sun bayyana yadda ake almabaranci da dukiyar kasar

''Abin kunya na ci gaba da rufeta game da rashin kimar kasar a idanun kasashen duniya kan yadda shugabanni ke karkatar da tunanin alummar kasar domin yin watanda tare da barnata da kudin Najeriya amma su ke nuna halin ko in kula game da illar abinda zai iya biyo baya'', in ji Afenifere

Kungiyar ta yi zargin cewa akwai rashin sanin yakamata kan yadda ake barin talakawan kasar cikin kunci da kuma matsalolin tafiyar da alumaran mulkin kasar ba tare da bin kaida ba.