Waiwaye: Mayar wa fadar shugaban ƙasa martani kan zaɓen 2027 da rikicin masarautu a Adamawa

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Ƴan arewa su jira zuwa 2031 domin mulkin Najeriya - Akume

George Akume

Asalin hoton, X/Akume

Sakataren gwamnatin tarraya, Sanata ya buƙaci ƴan siyasa daga arewacin ƙasar da ke neman tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 su jira har sai 2031.

A cewarsa, lokacin shugaba Bola Tinubu ya kammala wa'adi na biyu na shugabancin Najeriya.

Akume a hirarsa da gidan talabijin na TVC, ya ce daga kudancin Najeriya ne ya kamata a fitar da shugaban ƙasa a 2027.

"Shugaba Tinubu ɗan kudanci ne, kuma a bar shi ya kammala wa'adinsa na biyu. Duk wanda ke neman mulkin ƙasar daga arewa a 2027 ya jira zuwa 2031," in ji Akume.

Ya ƙara da cewa ya kamata a bar ƴan kudu su yi mulki na shekara takwas daga nan sai a koma arewa. 'Idan ba haka ba za a lalata ƙasar nan.'

Tun bayan da gwamnatin Tinubu ta soma yunƙurin yi wa dokar harajin ƙasar garan-bawul, gwamnatinsa ke fuskantar adawa daga arewacin ƙasar.

Kowane ɗan Najeriya na da damar takarar shugaban ƙasa a kowane lokaci - Atiku

Tsohon mataimkin shugaban Najeriya

Asalin hoton, Atiku Abubakar

Wasu kalamai da suka fito daga bakin sakataren gwamnatin Najeriya, George Akume, na neman ƴan siyasar arewacin ƙasar su jira har shekarar 2031 idan suna son yin takarar shugabancin ƙasar, sun janyo cece-kuce.

Mista Akume, ya faɗi hakan ne yayin hira da wani gidan talabijin a ƙasar, inda ya ce kamata ya yi a bar yankin kudancin Najeriya ya karasa shekaru takwas ɗin sa, kamar yadda itama Arewa ta yi lokacin mulkin shugaba Buhari.

Kalaman dai sun girgiza ƴan siyasar arewacin Najeriya, inda tuni aka fara mayar da martani.

Mai magana da yawun tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, Abdulrashid Shehu Uba, ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowaye damar fita don neman kujerar shugaban ƙasa.

Shettima ya soki sabuwar shugabar jam'iyyar Conservative a Birtaniya saboda kaskantar da Najeriya

Kashim Shettima

Asalin hoton, KASHIM SHETTIMA/FACEBOOK

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya soki sabuwar zaɓabɓiyar ƴar shugabar jam'iyyar Conservative a Birtaniya, Kemi Badenoch saboda kaskantar da Najeriya.

Shettima ya bayyana haka ne ranar Litinin a taron tattaunawa kan hijira karo na 10 da aka yi a Abuja.

Mataimakin shugaban Najeriyar ya ce "Muna alfahari da kasancewar Kemi Badenoch a matsayin shugabar jam'iyyar Conservative a Birtaniya, duk da kaskantar da ƙasarta ta asali da ta ke yi."

"Tana da damar bayyana ra'ayinta a kan koma mene ne, kai har ma idan tana son cire Kemi a cikin sunanta ma za ta iya, to amma ba wai hakan ba zai rage wa Najeriya matsayinta na kasancewa ƙasar baƙar fata mafi shahara ba."

Ya ce, "Idan ka lura duk inda ka samu baƙar fata uku to ko shakka babu za ka ga ɗaya daga cikinsu ɗan Najeriya ne."

Mahalisar dokokin Adamawa ta amince da karɓa-karɓar shugabanci tsakanin sarakunan jihar

Ahmadu Umaru Fintiri

Asalin hoton, Ahmadu Umaru Fintiri/Facebook

Majalisar dokokin jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya ta amince da ƙudurin dokar kafa masarautu uku masu daraja ta ɗaya a jihar.

Amincewa da ƙundirin - wanda a yanzu ke jiran sa hannun gwamnan jihar, Ahmadu Finitiri - na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan gwamnan ya sa hannu kan wata dokar ta ƙirƙirar sabbin gundumomin hakimai 84 da aka yi ranar 4 ga watan Disamba.

A wata wasiƙa da gwamna da aika wa majalisar, a farkon mako ya buƙaci ƴanmajalisar su amince da ƙudirin naɗa wa da cire sarakuna a jihar, wadda za ta ba gwamnan damar ƙirƙirar sababbin masarautu da naɗa sarakuna ko kuma cire su.

Kotu ta bayar da belin Yahaya Bello

Yahaya Bello

Asalin hoton, Yahaya Bello/Facebook

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello kan kuɗi naira miliyan 500.

A zaman da kotun ta yi a ranar Juma'a ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Emeka Nwite, kotun ta buƙaci ya gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa domin samun belin.

Alƙalin ya ce dole ne mutanen da za su tsaya masa su kasance sun mallaki kadarori a Abuja, babban birnin ƙasar.

Haka kuma kotun ta ce dole ne masu tsaya masa su gabatar wa kotun takardun kadarorin nasu domin tantancewa.

A baya-bayan nan ne dai hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta gurfanar da tsohon gwamnan na Kogi a gaban kotu bisa zarge-zarge 19 da suka ƙunshi almundahanar kuɗaɗe da yawansu ya kai naira biliyan 80.

An yi wa matata tiyatar gyara fuska a Netherland - Tijjani Babangida

Tijjani Babangida da matarsa Maryam Waziri

Asalin hoton, Maryam Waziri

Tsohon ɗan ƙwallon Najeriya, Tijjani Babangida ya ce matarsa, Maryam Waziri ta rasa idonta guda ɗaya kuma an yi mata tiyatar gyaran fuska a Netherlands.

A ranar 9 ga watan Mayu ne wani mummunan hatsarin mota ya rutsa da Babangida da iyalansa ciki har da ƙaninsa da matarsa da ɗansa mai shekara ɗaya da rabi, a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria.

Cikin wata hira da ya yi da tsohuwar ƙungiyarsa ta Ajax Amsterdam a Netherland, Babangida ya ce damuwar da ya shiga ba za ta taɓa gushewa ba.

Maryam Waziri - wadda tauraruwa ce a masana'atar shirya fina-finai ta Kannywood - ta auri tsohon ɗan ƙwallon ne a watan Nuwamban 2021.

Ƙaninsa Ibrahim Babangida ya mutu nan take bayan hatsarin, yayin da ƙaramin ɗansa, mai suna Fadil ya rasu kwanaki bayan hatsarin, sannan mai aikin gidansu ta samu karaya a ƙafa.

Ba za a daina amfani da tsofaffin takardun naira ba - CBN

Takardun naira

Asalin hoton, Getty Images

Babban bankin Najeriya CBN, ya ce ba za a daina amfani da tsofaffin takardun kuɗi na naira 1000 da 500 da 200 ba.

A wata sanarwa da babban bankin ya fitar, wanda muƙaddashin daraktan hulɗa da jama'a na bankin Sidi Ali Hakama ta fitar, bankin ya ce labarin da ake yaɗawa kan wa'adin amfani da tsofaffin takardun kuɗin ba haka ba ne, inda ta ƙara da cewa babu ranar da za a daina.

Bankin ya kuma yi kira ga jama'a su yi watsi da raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa daga ranar 31 ga watan Disamban 2024, za a daina amfani da tsofaffin kuɗin.

"Hukuncin da Kotun Ƙolin Najeriya ta yanke a ranar 29 ga Nuwamban 2023, ta amince a ci gaba da amfani da sababbi da tsofaffin takardun kuɗaɗen naira," kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.