Farin ciki, bikin cika shekara 118 a duniya, kayan kawa na cakulat a cikin hotunan Afirka na mako

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Wasu daga cikin fitattun hotunan Afirka na mako;

Wani mutum na kallon zanen wata mace 'yar siyasa  a ranar Litinin, 30 Satumba 2024

Asalin hoton, JOSE COELHO / EPA

Bayanan hoto, Mako guda gabannin babban zabe a kasar Mozambique, a ranar litinin dukkan titinan birnin Chimoio sun cika da hotunan 'yan takara na jam'iyyu daban-daban.
'Yan mata sun tsaye a kusa da wata mota launin Ja, a ranar Lahadi 29 Satumba 2024

Asalin hoton, GERALD ANDERSON / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A ranar Lahadi, wata motar 'yan kwalisar zamanin da kenan a wurin wani taro a birnin Nairobi na Kenya. Ta ja hankulan mutane da masu gasa daga sassa daban-daban na Afirka.
Mai tallan kayan kawa sanye da rigar da aka yi da cakulet, da launin tutar kasar Ivory Coast.

Bikin na hadin gwiwa ne tsakanin kamfanin cakulet na kasar mai suna chocolatier Viviane Kouame da fitacciyar mai kayan ta Ivory Coast, Gilles Toure -Asabar 28 Satumba 2024

Asalin hoton, LUC GNAGO / REUTERS

Bayanan hoto, A ranar Lahadi a kasar Ivory Coast , wata mai tallan kayan kawa sanye da rigar da aka yi da Cakulet a ranar bikin Cocoa da Cakulet.
Mai tallan kayan kawa sanye da tufafin da fitaccen mai dinkin nan  Mzukisi Mbane ya samar - Abasar 28 Satumba 2024

Asalin hoton, LEFTY SHIVAMBU / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, An fara makon tallan kayan kawa a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu ...
Mata masu tallan kayan kawa na tafiya da rangaji tamkar Dawisu, sanye da tufafin da mai kayan kawa na Afirka ta Kudu Mzukisi Mbane ya samar, a ranar Asabar 28 Satumba 2024

Asalin hoton, LEFTY SHIVAMBU / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Anan ma dai kayan da fitaccen madinkin nan Mzukisi Mbane ya samar ne...
Mai tallan kayan kawa sanye da takalmin kamfanin Essie Apparel, wanda Enhle Mbali ya samar, a ranar Lahadi 28 Satumba 20224

Asalin hoton, LEFTY SHIVAMBU / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Wadannan takalman ne da kamfanin Essie Apparel da Enhle Mbali ya samar.
Mai gyaran mota a bakin aiki, a gefe guda kuma ga tarin karafan da ake iya sake sarrafa su a ranar Juma'a 27 Satumba 2024

Asalin hoton, GERALD ANDERSON / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Wani mai gyaran mota kenan a bakin aiki a ranar Juma'a a birnin Nairobi na kasar Kenya.
Direban tasi ya leko da kan shi daga cikin mota a ranar Talata 1 Oktoba 2024

Asalin hoton, ADEKUNLE AJAYI / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A ranar Talata wani direban Tasi ne ya ke daga murya domin nuna goyon baya ga masu zanga-zanga da suka gaji da hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa a Najeriya.Sun fito titunan birnin Lagos, a ranar 1 ga watan Oktoba, ranar da ake bikin cikar Najeriya shekaru 64 da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya.
Maza na cashewa a ranar Lahadi 29 Satumba 2024

Asalin hoton, OLYMPIA DE MAISMONT / AFP

Bayanan hoto, Gabannin wannan ranar a dai birnin Lagos, mutane da dama sun sha shagalin Kalankuwar unguwar 'yan rabbana ka wadata mu...
Makadin badujala a bakin aiki, sanye da tufafi launin kore da fari wato tutar Najeriya, 29 Satumba 2024.

Asalin hoton, OLYMPIA DE MAISMONT / AFP

Bayanan hoto, Makadanda suka cashe a wurin bikin kalankuwar, sun ce sun yi hakan ne domin sauya tunanin wadanda ke kallon mazauna yankunan rabbana ka wadata mu a Najeriya.
Jerin gwanon Zalbe a cikin ruwa, a wurin shakatawa na  Nakuru a ranar Asabar 28 Satumba 2024

Asalin hoton, JAMES KAMAU WAKIBIA / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Jerin gwanon Zalbe a cikin ruwa, a wurin shakatawa na Nakuru a ranar Asabar
 Dawa ta yi kyau, mafarauci ya kama tsuntsu  2 Oktoba 2024

Asalin hoton, ALI MOUSTAFA / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A ranar Laraba a birnin Alkhahira na Masar wata mafarauci ne ya kama tsuntsun da zai gasa domin ya ce. Sai dai masu rajin kare tsuntsaye na sukar matakin farautarsu da ake yi, da bayyana muhimmancin alkinta irin tsuntsayen, amma mazauna kauyuka sun ce cin tsuntsayen ya zama dole matukar ana son kai abinci bakin salati.
mawakiya 'yar Najeriya Ayra Starr ce ta kwame domin daukar hoto, a otal din  Shangri-La Hotel a Faris - Asabar 28 Satumba 2024

Asalin hoton, GEOFFROY VAN DER HASSELT / AFP

Bayanan hoto, Can a kasar Faransa kuwa a ranar Asabar, mawakiya 'yar Najeriya Ayra Starr ce ta kwame akan jar dardumar karrama wadanda suka halarci makon kayan kawa a birnin Faris na kasar Faransa.
Marubuciya kuma mawakiya Fatoumata Diawara ta na waka, Asabar  28 Satumba 2024

Asalin hoton, OUPA BOPAPE / EPA

Bayanan hoto, Shahararriyar mawakiyar nan 'yar Mali, Fatoumata Diawara a bakin aiki, lokacin kalankuwar mawaka masu salon Jazz da aka yi a Sandton, da ke Afirka ta Kudu a ranar Asabar.
'Yar wasan tsere Milkesa Mengesha ranar Lahadi 29 Satumba 2024

Asalin hoton, JOHN MACDOUGALL / AFP

Bayanan hoto, 'Yar wasan tsereta kasar Habasha Milkesa Mengesha ta yanke jiki ta fadi, lokacin da ta yi nasara a gudun yada kanin wani a kasar Jamus ranar Lahadi.
Wata mace ke sheka kuka sakamkon mutuwar 'yan uwanta a kifewar kwale-kwalen ranar Alhamis 3 Oktoba 2024

Asalin hoton, REUTERS

Bayanan hoto, 'Yan uwan wadanda suka mutu a kifewar kwale-kwale, lokacin da suke zantawa da 'yan jarida a ranar Alhamis.Kwale-kwalen ya nutse a kogin Kivu a kusa da tashar ruwa ta Kituku a Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo.
A ranar Laraba a babban birnin kasar Mali Bamako, wani yaro zaune a cikin kwale-kwale a wani yanki da akai ambaliyar ruwa 2 Oktoba 2024

Asalin hoton, OUSMANE MAKAVELI / AFP

Bayanan hoto, A ranar Laraba a babban birnin kasar Mali Bamako, wani yaro zaune a cikin kwale-kwale a wani yanki da akai ambaliyar ruwa
Mata sanye da tufafi iri daya, su na rawa da waka a ranar Laraba 2 Otoba 2024

Asalin hoton, BRIAN OTIENO / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Mazauna yankin Leribe a Lesotho, su na rawa da wakar tarbar Yarima Harry na masarautar Birtaniya, da tawagar kwararru da suka je ziyarar gani da ido kan yadda ake fama da sauyin yanayi.
Wata mata na yi wa yarinya kitso a kasuwa, inda suke saida gyaada a ranar Litinin 30 Satumba 2024

Asalin hoton, RICCI SHRYOCK / AFP

Bayanan hoto, A ranar Litinin, mai saida gyada a kasuwar Bissau da ke Guinea-Bissau.
Wani magidanci mai shekara 35, dauke da dan shi ya na ma sa wasa a birnin Bujumbura, na kasar Burundi - Talata 1 Oktoba 2024

Asalin hoton, EVRARD NGENDAKUMANA / REUTERS

Bayanan hoto, A ranar Talata Eric Manigaba ne ke wasa da dan shi, bayan an sallamo shi daga asibiti sakamakon jinyar da ya yi ta cutar Kyandar Biri. Mutane na tsangwamar wadanda suka kamu da cutar ko da sun warke a kasar Burundi.
Margaret Maritz mai shekara 118 tare da 'ya'yanta mata biyu, Getryda Maritz, mai shekara 81, da kuma Liza Daniels, mai shekara 67 - Juma'a 27 Satumba 2024

Asalin hoton, ESA ALEXANDER / REUTERS

Bayanan hoto, A ranar Juma'a a Afirka ta Kudu, a kuma yankin Western Cape, tsohuwa Mararet Maritz kenan ke bikin cika shekara 118 a duniya.