Dabarar sirri da Hamas ke amfani da ita wajen biyan ma'aikatanta albashi

    • Marubuci, Rushdi Abualouf
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Gaza correspondent in Istanbul
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Bayan kusan shekara biyu ana yaƙi, an yi mummunar illa ga ɓangaren soji na Hamas yayin da ɓangaren siyasa na ƙungiyar kuma ke cikin matsi.

Amma duk da haka, Hamas ta ci gaba da amfani da wani tsarin sirri na biyan kuɗi wajen biyan ma'aikatanta albashi a tsawon wannan lokaci, inda aka ƙiyasta ta biya ma'aikatanta 30,000 kuɗin albashi kimanin dala dala miliyan bakwai.

BBC ta tattauna da wasu ma'aikatan gwamnatin Hamas biyu, waɗanda suka tabbatar cewa an biya su kimanin dala 300 kowanne a cikin makon da ya gabata.

An yi yakinin cewa suna cikin dubban ma'aikatan Hamas da ke samun kimanin kashi 20 cikin ɗari na albashin da aka saba biyan su cikin kowane mako 10.

Yayin da ake cikin mummunan tashin farashin kayan masarufi, ɗan albashin da ake biya - na haifar da ƙiyayya tsakanin ƴaƴan jam'iyyar.

Mummunan ƙarancin abinci - wanda hukumomin agaji ke ɗora laifin kan toshe hanyoyin da Isra'ila ta yi - da matsananciyar yunwa da ake fama da ita sun ƙara tayar da farashin kaya fiye da kowane lokaci a tarihi.

Kasancewar aikin banki ya durƙushe a Gaza, hatta samun albashi ya zama wani abu mai matuƙar sarƙaƙiya kuma mai hatsari. A lokuta da dama Isra'ila na yin leƙen asiri domin ganowa da kuma kai farmaki ga tsarin tura kuɗaɗen albashi na gwamnatin Hamas, a ƙoƙarin Isra'ilar na haifar da cikas ga ayyukan ƙungiyar.

Ma'aikata, kamar ƴansanda da kuma ma'aikatan haraji kan samu saƙo na basaja a wayoyinsu ko wayoyin matansu da ke cewa su je wani wuri a wani takamaiman lokaci domin "su hadu da abokai su sha shayi".

A wurin da aka ayyana, ma'aikacin zai ga wani mutum ko kuma wata mace ta zo wurinsa kai-tsaye ta miƙa masa ambulan ƙunshe da kuɗi, daga nan sai ta juya ba tare da cewa uffan ba.

Wani ma'aikacin ma'aikatar harkokin addini ta Hamas, wanda bai so a bayyana sunansa ba saboda dalilai na tsaro ya bayyana hatsarin da suke shiga wajen karɓar albashin.

"Duk lokacin da zan je karɓar albashi nakan yi ban-kwana da matata da yarana. Kasancerwar na san wata ƙila ba zan iya komawa gida ba," in ji shi.

"A lokuta da dama Isra'ila kan kai hari a wajen da ake bayar da albashin. Na sha da ƙyar a ɗaya daga cikin irin wadannan hare-hare da aka kai a wata kasuwar Birnin Gaza mai cike da hada-hada."

Alaa, wanda muka ɓoye sunansa bisa dalilai na tsaro, malamin makaranta ne da gwamnatin Hamas ta ɗauka aiki, kuma shi kaɗai ne ke da hanyar samun kuɗin shiga a cikin iyalinsa, su shida.

"Na karɓi shekel 1,000 (kimanin dala 300) na tsofaffin takardun kuɗi - babu wani ɗan kasuwa da zai karɓe su. Shekel 200 kacal na iya kashewa - sauran kuwa, a gaskiya ban san yadda zan yi da su ba," kamar yadda ya shaida wa BBC.

"Bayan shafe wata biyu da rabi muna fama da yunwa, suka biyu mu albashi da lalatattun kuɗi.

"Akan tursasa min zuwa wuraren da ake rabon abinci da sa ran kila zan samu garin yin burodin da zan iya ciyar da ƴaƴana. Wani lokaci nakan samu ɗan ƙalilan, amma a mafi yawan lokuta ba na samun komai."

A watan Maris sojojin Isra'ila sun ce sun kashe shugaban sashen kuɗi na ƙungiyar Hamas, Ismail Barhoum, a wani hari da suka kai a asibitin Nasser da ke Khan Younis. Sun zarge shi da tura wa ɓangaren soji na Hamas kudi.

Babu tabbas kan yadda Hamas ke samun damar biyan ma'aikatanta albashi ganin yadda aka lalata akasarin gine-ginen gudanar da mulkinta da kuma tsarin samun kuɗaɗenta.

Daya daga cikin manyan jami’an Hamas wanda ya rike mukamai masu girma kuma yake da masaniya kan harkokin kudi na kungiyar, ya shaida wa BBC cewa Hamas ta adana tsabar kudi kimanin dala miliyan 700 da daruruwan miliyoyin takardar kudi na Shekel a hanyoyin karkashin kasa gabanin harin da ta kai wa Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, lamarin da ya haifar da yakin da ake fama da shi.

Ana da yakinin cewa kudaden na karkashin ikon tsohon shugaban kungiyar Yahya Sinwar ne da kuma dan’uwansa Mohammed - wadanda duk Isra’ila ta riga ta kashe su.

Fusata kan taimaka wa magoya bayan Hamas

A tarihi, hanyar samun kudin Hamas ta dogara ne kan harajin da ake tatsa daga al’ummar Gaza wanda ake laftawa kan kayan masarufi da ake shiga da su yankin daga waje, sai kuma tallafin da take samu daga Qatar.

Dakarun Qassam Brigades, wato bangaren soji na Hamas kuwa na samun kudin da take gudanar da ayyukanta ne yawanci daga Iran.

Wani babban jami’in kungiyar Muslim Brotherhood ta Masar, daya daga cikin kungiyoyin masu ikirarin kishin Musulunci mafiya tasiri a duniya, ya ce suna ware kashi 10 cikin dari na kasadin kudinsu ne don tallafa wa Hamas.

A yunkurin ci gaba da samun kudi a lokacin da ake yaki, Hamas ta cigaba da dora haraji kan ‘yan kasuwa sannan kuma ta rika sayar da tabar sigari kan farashi mai tsada, sun nunka asalin kudinta sau 100.

Kafin barkewae yakin ama sayar da kwalin sigari na kunshe da kara 20, ana sayar da shi ne kan dala 5 - amma a haka sai da farashinta ya kai sama da dala 170.

Baya ga yin amfani da kudi wajen biyan albashi, Hamas ta kuma rika raba abinci ga ma’aiktanta ta hanyar kwamitocin kai dauki na cikin gida, wanda aka yi ta saiya shigabancinsa sanadiyyar hare-haren Isra’ila.

Wannan ya fusata al’umma, inda mutane da dama suka zargi Hamas da raba wa ‘ya’yanta kawai tallafi a maimakon dukkanin al’umma.

Isra’ila ta zargi Hamas da sace kayan agajin da ake shiga da shi Gaza a lokacin da aka samar da yarjejeniyar tsagaita wuta a farkon wannan shekara, wani abu da Hamas ta musa. Sai dai wasu majiyoyi sun shaida wa BBC cewa Hamas ta debi wani bangare na agajin da aka rika kai wa yankin.

Wata mata, wadda mijinta ya mutu shekara biyar da suka gabata sandiyyar cutar kansa, kuma take kula da yara uku, Nisreen Khaled, ta shaida wa BBC cewa: “Lokacin da yunwa ta tsananta, ‘yayana sukan yi ta kuka, ba saboda yunwa kawai ba, har ma saboda yadda suke kallon makwaftanmu masu alaka da Hamas na karbo buhunan garin fulawa.

“Shin ba su ne dalilin fadawar mu cikin wannan matsala ba? Me ya sa ba su tanadi abinci da ruwa da kuma magani ba kafin kadfamar da harin na ranar 7 ga watan Oktoba.