Waiwaye : Amincewa da kasafin kuɗi da ɓatan bindigogi a Najeriya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi

Majilisar dokokin Najeriya ta amince da kasafin kuɗin ƙasar na 2025

A ranar Alhamis ne Majalisun dokokin Najeriya suka amince da ƙudirin kasafin kuɗin ƙasar na shekarar 2025 na naira tiriliyan 54.99.

Kasafin wanda ke ƙunshe da kasafin kuɗaɗen yau da kullum da manyan ayyuka da biyan bashi da kuma hasashen samun kuɗin da za a cike giɓin kasafin kuɗin kamar haka:

Kasafi hukumomi da ma'aikatu: Naira tiriliyan 3.65

Kuɗaɗen gudanarwar gwamnati: Naira tiriliyan 13.64

Kuɗaɗen manyan ayyuka: Naira tiriliyan 23.96

Kuɗaɗen biyan bashi: Naira tiriliyan 14.32

Giɓin da ke cikin kasafi: Naira tiriliyan 13.08

A ranar 5 ga watan Fabarairu ne Shugaba Tinubu ya ƙara yawan kuɗin kasafin na 2025 daga naira tirirliyan 49.7 zuwa naira tiriliyan 54.2, bisa dalilan samun ƙarin yawan kuɗaɗe da hukumomi suka samar wa gwamnati.

Muna roƙon majalisa ta gudanar da binciken ɓatan bindigogi na gaba a sirri - Sufeto Janar

A ranar Alhamis ne majalisar dattawan Najeriya ta gabatar da wata wasika daga Sifeto Janar na ƴansandan ƙasar, Kayode Egbetokun wadda a ciki yake roƙon majalisar kan cewa a gudanar da zama na gaba na jin bahasi dangane da ɓatan wasu dubban bindigogi har 3,907, cikin sirri, bisa dalilan tsaro.

Sai dai a wasiƙar, Sufeto Janar ɗin ya yi watsi da rahoton 2019 da ofishin babban mai bincike na gwamnatin tarayya ya fitar wanda ya yi iƙirarin ba a san inda dubban bindigogin ƴansanda suka shiga ba ya zuwa watan Janairun 2020 inda ya bayyana rahoton da cewa cike yake da kurakurai.

An karanta wasiƙar ne sa'a 48 bayan wani zaman saurare da kwamitin majalisar dattawan mai binciken kashe-kashen kuɗaɗen gwamnati ya yi inda rundunar ƴansandan ta yi ta nuƙu-nuƙu wajen kare kanta kan ɓatan bindigogin.

Gwamatin Najeriya ta yi ƙarin kuɗin kafa jami'o'i

A ranar Litinin da ta gabata ne gwamantin Najeriya ta sanar da ƙara kudin samun lasisin kafa jami'a a ƙasar daga naira miliyan 5 zuwa naira miliyan 25.

Haka kuma gwamantin ta ƙara kuɗin siyen fom ɗin kafa jami'ar daga naira miliyan ɗaya zuwa miliyan biyar.

Shugaban hukumr kula da jami'ao'in Najeriya, NUC, Farfesa Abdullahi Ribadu ne dai ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar ta Litinin.

Hukumar ta NUC ta ce matakin ƙarin na daga cikin ƙoƙarin da suke yi na sake fasalin yadda ake kafa jami'o'in kuɗi a Najeriya, don ganin suna biyan buƙatun 'yan ƙasar, da haɓaka cigaban ilimi a jami'o'in.

Najeriya ce ta 140 cikin jerin ƙasashen da aka fi tafka rashawa a duniya

A ranar Talatar da ta gabata ne, ƙungiyar Transparency International ta fitar da wani rahoto da ke nuna cewa Najeriya ta zama ƙasa ta 140 a cikin jerin ƙasashen da aka fi cin hanci da rashawa a duniya a shekarar nan ta 2024.

A cikin rahoton, Transparency ta ce Denmark ce ƙasar da ta kasance wadda ba ta fuskantar matsalar ta cin hanci da rashawa.

Rahoton wanda ya yi nazari kan ƙasashe 180 na duniya ya yi amfani da masana da ƴan kasuwa wajen tantance matsayin kowace ƙasa.

Transparency International ta ce Najeriya tare da wasu ƙasashe kamar Uganda, Mexico, Madagascar, Iraq da Kamaru sun samu maki 26 ne cikin 100.

Sudan ta Kudu da Somaliya da kuma Venezuela na cikin ƙasashen da aka fi tafka rashawa a duniya.

Majalisa ta gayyaci shugaban hukumar Kwastam kan ƙin yi wa wasu ritaya

A ranar Talatar da ta gabata ne kwamitin majalisar wakilan Najeriya, da ke karbar koken al'umma ya gayyaci shugaban hukumar Kwastam, Adewale Adeniyi da ya bayyana a gabansa kafin ranar Talatar mako mai zuwa.

Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewar, Chooks Oko, ya ce tilas ne Adeniyi ya bayyana a gaban kwamitin don ya kare kansa daga wani koke da ake yi a kansa na kin yi wa wasu jami'an hukumar ritaya, duk da cewar lokacin barinsu aiki ya cika.

Gidauniyar Obasi-Pherson ce dai ta shigar da koken ta gaban majalisar ta, inda suka yi zargin cewar mataimakan kontirola da lokacin ajiye aikinsu ya yi har yanzu sun ki ajiyewa.

Majalisar Wakilan Najeriya ta buƙaci a janye ƙarin kuɗin kiran waya da na data

Haka kuma a ranar Talatar ne majalisar wakilan Najeriya ta buƙaci hukumar da ke kula da kamfanonin sadarwa ta ƙasar, NCC ta janye karin kuɗin kira da na data da kamfanonin sadarwar suka yi.

Ƙarin kuɗin kiran na kashi 50 cikin 100 da Kamfanonin sadarwar suka yi ya soma aiki cikin makon nan.

Hakan ne ma ya sa jama'a suke ta kokawa da ƙarin yayin da ƙungiyar ƙwadago ma ta ƙasar NLC ta buƙaci jama'a da su ƙaurace wa kamfanonin sadarwar don nuna fushinsu a kan ƙarin kuɗin.

Majalisar wakilan ta ce yin ƙari a wannan lokacin ba adalci ba ne saboda ƴanƙasar na cikin matsin rayuwa.

To amma kamfanonin sadarwar na cewa sun yi ƙarin ne wanda ya zamar musu dole a cewarsu sakamakon tsadar gudanar da ayyukansu musamman man dizil da suke amfani da shi a injinansu.

Kundin Guinness ya karrama ɗan Najeriya kan bajintar ɗaukar hoto

A ranar Laraba ne Kundin Adana Abubuwan Bajinta na Duniya, 'Guinness World Record ' ya karrama wani ɗan Najeriya, ɗan asalin jihar Yobe, Saidu Abdulrahman saboda ɗaukar ƙananan hotuna masu yawa cikin sa'a guda.

Wakilan kundin sun gabatar da lambar karramawar ne ga gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni a gidan gwamnatin jihar da ke Damaturu, a ranar Larabar.

Sa'idu Abdulrahman ya samu wannan bajinta ne a shekarar da ta gabata, bayan da ya ɗauki ƙananan hotuna 897 a cikin mintuna 60.

Gwamnan Mai Mala Buni ya ce yana alfahari da bajintar matashin, wanda ya ce yana fatan hakan zai zaburar da sauran matasan jihar.