Champions League: Real Madrid ta kasa kai wa zagayen gaba kai tsaye

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid za ta buga wasannin cike gurbi a Champions League, watakila a haɗa ta da Manchester City ko kuma Celtic.
Ƙungiyar Sifaniya ta yi nasarar doke Brest 3-0 ranar Laraba a Faransa a wasa na karshe a cikin rukuni.
Duk da doke Brest da Real Madrid mai rike da kofi ta yi, ya sa ta kasa samun gurbin shiga zagayen gaba kai tsaye, har sai ta yi karawar cike gurbi.
Rodrygo ne ya ci biyu da kuma Jude Bellingham da ya zura ɗaya a raga a wasan na babbar gasar zakarun Turai ta bana da aka sauya wa fasali.
Kenan Real Madrid za ta buga fafatawar cike gurbi gida da waje, sannan ta samu damar kai wa zagayen ƴan 16 da za a ci gaba da wasannin Champions League.
Itama Brest ta samu zuwa fafatawar cike gurbin, duk da cewar wannan shi ne karon farko da ta shiga babbar gasar ta zakarun Turai.
Tun farko an tsara cewar duk ƙungiyar da take cikin ƴan takwas ɗin farko, sun samu tikitin shiga zagaye na biyu na ƴan 16 kai tsaye.
Daga mataki na tara zuwa na 24 za a haɗa su wasannin cike gurbi, domin zakulo takwas ɗin da za su kai zagayen gaba.
Sakamakon wasannin da aka buga:
- Aston Villa 4 - 2 Celtic
- Barcelona 2 - 2 Atalanta
- Bayer Leverkusen 2 - 0 Sparta Prague
- Bayern Munich 3 - 1 Slovan Bratislava
- Borussia Dortmund 3 - 1 Shakhtar Donetsk
- Brest 0 - 3 Real Madrid
- Dinamo Zagreb 2 - 1 AC Milan
- Girona 1 - 2 Arsenal
- Inter Milan 3 - 0 Monaco
- Juventus 0 - 2 Benfica
- Lille 6 - 1 Feyenoord
- Manchester City 3 -1 Club Brugge
- PSV 3 - 2 Liverpool
- Red Bull Salzburg 1 -4 Atlético Madrid
- Sporting CP 1 - 1 Bologna
- Sturm Graz 1 - 0 RB Leipzig
- Stuttgart 1 - 4 PSG
- Young Boys 0 - 1 Red Star Belgrade












