Ya kamata mu koma kan ganiya daga wasan Feyenoord - Guardiola

Asalin hoton, Getty Images
Pep Guardiola ya bukaci ƴan wasan Manchester City su kara sa kaimi a wasan da zasu kara a Champions League da Feyenoord ranar Talata.
City na fatan komawa kan ganiya, bayan da take fuskantar kalubale a dukkan karawar da take yi a baya-bayan nan.
Ranar Asabar Tottenham ta je ta doke City 4-0 a Etihad a Premier League karo na biyar da ta yi rashin nasara a jere a dukkan fafatawa.
Karon farko da Guardiola ya sha kashi a wasa biyar a jere, tun bayan da ya fara aikin horar da tamaula a tarihi.
Kuma karon farko da City ta yi rashin nasara biyar a jere tun bayan Afirilun 2006, kuma karo na uku a jere da aka doke ta a Premier League.
Da wannan sakamakon City mai maki 23 tana da tazarar maki takwas tsakaninta da Liverpool, wadda ke jan ragama, bayan cin Southampton 3-2 ranar Lahadi.
Ƙungiyar da ke Etihad na fama da masu jinya da suka haɗa da wanda ya lashe ƙyautar Ballon d'Or, Rodri da Ruben Dias da Mateo Kovacic.
Sauran sun haɗa da Jeremy Doku da kuma Oscar Bobb, yayin da Kevin de Bruyne ya murmure.
Guardiola, wanda ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da horar da tamaula a City kaka biyu, ya lashe kofi 18 a Etihad har da Premier League shida da Champions League.
City tana ta 10 daga ƙungiya 36 a teburin Champions League da maki bakwai daga karawa huɗu, Feyenoord kuwa tana ta 21 a teburin.











