Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Liverpool ta fara Premier League ta bana da kafar dama
Diogo Jota da Mohamed Salah ne suka ci wa Liverpool ƙwallayen da ta doke Ipswich Town a wasan farko da Arne Slot ya ja ragama a Premier League.
Ipswich Town, wadda ta koma buga babbar gasar tamaula ta Ingila a bana, ta karbi bakuncin ƙungiyar Anfield a Portman Road a karawar makon farko.
Jota ɗan wasan tawagar Portugal ya ci ƙwallon ne, bayan raba tamaula da ya yi tsakaninsa da Salah da Trent Alexander-Arnold a zagaye na biyu.
Minti biyar tsakanin Salah ya kara na biyu, bayan da ya samu tamaula ta hannun Dominik Szoboszlai, karo na tara da ɗan kasar Masar kan ci ƙwallo a wasan farko.
Wannan shi ne karon farko da Ipswich ta koma buga Premier League tun bayan shekara 22 da ta faɗi daga gasar.
Haka kuma wannan ne karon farko da Ipwich Town ta yi rashin nasara a gida bayan kusan wata 12.
Ranar 24 ga watan Agusta, Ipswich za ta ziyarci Manchester City a karawar mako na biyu a Etihad.
Ita kuwa Liverpool za ta karɓi bakuncin Brentford a fafatawar mako na biyu a babbar gasar tamaula ta Ingila a Anfield.