Abin da ya sa gwamnati ta hana kafa ƙarin manyan makarantu

Tinubu

Asalin hoton, Presidency

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Gwamnatin Najeriya ta sanya takunkumin kafa ƙarin manyan makarantu a faɗin ƙasar har na tsawon shekaru bakwai.

Takunkumin ya haɗa da jami'o'i na gwamnati da kwalejojin ilimi.

Ministan ilimin Najeriya, Tunji Alausa wanda ya sanar da haramcin ya ce gwamnati ta ɗauki matakin ne bisa la'akari da matsaloli da dama da kafa irin waɗannan manyan makarantu ke tattare da su.

An cimma wannan sabuwar ƙa'idar ne a yayin zaman majalisar zartarwa da Shugaba Tinubu ya jagoranta a ranar Laraba.

Najeriya dai na da jami'o'in gwamnati fiye da 60 da kuma kwalejojin ilimi fiye da 80 baya ga masu zaman kansu.

Dalilan da suka sa muka ɗauki mataki - Alausa

Ministan na ilimi na Najeriya, Tunji Alausa ya ce akwai manyan makarantun nan da yawa a Najeriya amma kuma ba sa aiki yadda ya kamata, inda ya ce wasun daga cikinsu ba su da cikakkun kayan koyo da koyarwa sannan wasu ma ɗaliban ba sa samun ilimin da suka je nema.

Ilimin da makarantun da dama ke samarwa ba shi da ingancin da ake buƙata.

Wasu manyan makarantun ba su da isassun ɗalibai sannan da dama daga irin waɗannan makarantu ba su da isassun malamai.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Da dama daga cikin jami'o'in gwamnati ba sa aiki yadda ya kamata, inda wasu kuma yawan ɗaliban da suke da su ya gaza 2,000."

Ministan ya kuma ƙara da bayar da misalin wata jami'a a arewacin Najeriyar da malamai suka fi ɗalibai yawa.

"A wata jami'a a arewacin Najeriya, tana da ma'aikata dubu ɗaya da ashirin inda kuma ɗaliban bai wuce 800 ba," in ji ministan.

Ya ƙara da cewa daga cikin jami'oi 350 da ake da su a Najeriya, akwai wadda ɗalibai 99 ne kawai suka nemi gurbi a cikinta.

Dangane da kwalejojin horas da malaman sakandire, ministan ya ce akwai waɗanda babu ɗalibin da ya nemi gurbi a cikinsu a jarrabawar JAMB da aka rubuta a baya-bayan nan.

Daga ƙarshe ministan ya ce idan har gwamnati ba ta ɗauki matakin gaggawa ba wajen dakatar da irin waɗannan makarantu ba to tsarin ilimi a ƙasar zai taɓarɓare.

"Lokaci ya yi na hana kafa ƙarin irin waɗannan makarantu domin hakan ya bai wa gwamnati damar kashe kuɗaɗe a kan waɗanda take da su a yanzu haka ta yadda za su dace da zamani.

Gwamnati ta makara - Dr Aliyu Tilde

Dr Aliyu Tilde wanda masani ne a harkokin ilimi kuma tsohon kwamishinan ilimi a jihar Bauchi, ya ce matakin da gwamnati ta ɗauka ya dace duk da ta yi fargar jaji.

"Ai duk wanda ya ɗebo da zafi bakinsa. An sha faɗa wa gwamnatin tarayya cewa jami'o'inmu da muke da su masu tarihi ya kamata a kula da su amma suka yi kunnen uwar shegu. Yanzu ga makarantun nan amma babu ɗalibai a cikinsu."

Dr Tilde ya ce yana goyon bayan gwamnati ta yi waiwaye dangane da jami'o'in da ake da su a Najeriya a yanzu haka bisa la'akari da yadda ake fitar da ɗaliban da ba su da ilimi mai nagarta.

"Ita da ma jami'a ai ba akafa ta domin ƙauye ba. A birane a kasan jami'o'i. Shi ne ma jami'ar. Saboda haka ƙoƙarin ƴansiyasa na kafa jami'o'i da makarantun gaba da sakandire a yankunansu ba cigaba ba ne." In ji Dr Tilde.