Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kalvin Phillips zai koma Ipswich a matsayin aro
Ɗan wasan Manchester City Kalvin Phillips na shirin komawa sabuwar ƙungiyar Ipswich Town a matsayin aro a kakar wasa ta bana.
Phillips ya kasa samun gurbi a tawagar City tun lokacin da ya bar Leeds United kan fan miliyan 45 shekaru biyu da suka gabata.
Ya koma West Ham a matsayin aro a kakar wasan da ta gabata a ƙoƙarinsa na ganin ya sami giurbi a tawagar Ingila na gasar Euro 2024 amma rashin kyawun yanayi gami da rauni ya hana shi samun shiga tawagar Gareth Southgate.
Yarjejeniyar aron da Ipswich ba ta haɗa da zaɓin mayar da ita ta dindindin.
Ko da yake kocin City Pep Guardiola ya yi magana sosai kan ɗan wasan mai shekara 28 a ziyarar da kulob ɗin ya kai Amurka, an bar shi a benci a wasan Community Shield da City ta fafata da Manchester United a ranar Asabar.
Kungiyoyi da dama ciki har da Fulham sun yi sha'awar siyan Phillips amma da alama Ipswich ta yi nasara a zawarcin, inda ake sa ran kammala cinikin da safiyar Juma'a.