Real Madrid na shirin karɓar bakuncin Milan a Champions League

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta kammala atisayen karshen mako a shirin da take na karɓar bakuncin Milan a Champions League ranar Talata a Santiago Bernabeu.
Ƴan wasan ƙungiyar sun fara da motsa jiki daga baya suka koma bani in baka da tamaula, sai suka koma gwada mai tsaron raga.
Daga baya aka tsuke filin aka raba tamaula tsakanin ƴan wasa, sannan aka kammala da sake gwada mai tsaron raga.
Har yanzu Courtois da Alaba da Carvajal suna jinya.
Rabon da Real ta yi wasa tun bayan da Barcelona ta doke ta 4-0 a El Clasico ranar 26 ga watan Oktoba a Santiago Bernabeu.
Kafin nan Real ta doke Borussia Dortmund 5-2 a Champions League ranar 22 ga watan Oktoba.
Bayan wasan da Real za ta karɓi bakuncin Milan a gasar zakarun Turai za ta yi wa Osasuna masauki a La Liga ranar 9 ga watan Nuwamba a Santiago Bernabeu.
Real ba ta buga wasan La Liga ba da Valencia a makon nan, sakamakon ambaliyar ruwa da ya shafi Sifaniya, inda abin ya yi muni a yankin Valencia.











