Ban taɓa aiki da ɗanwasa kamar Van Dijk ba - Slot

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kocin ƙungiyar Liverpool ta Ingila, Arne Slot ya ce ɗanwasan bayan ƙungiyar, Virgil van Dijk yana da matuƙar muhimmanci.

Slot ya bayyana haka ne a lokacin da yake bayyana farin cikinsa kan tsawaita kwantiragin da ɗanwasan ya yi a Liverpool.

Ya ce, "kwatanta yadda na ji zai yi wahala. Za ka gane irin muhimmancinsa ne idan yana cikin filin wasa. Yana taka rawa sosai wajen tsaron baya, da kuma taimakawa wajen rarraba ƙwallo zuwa gaba."

Slot ya ce bayan ƙwarewa wajen taka leda, van Dijk jagora ne a ciki da wajen filin ƙwallo.

"Jagora ne abin koyi a wajen atisaye. Ban taɓa aiki da wani ɗanwasan da ya iya jagoranci irinsa ba, da ma yadda yake ƙarfafa gwiwar sauran ƴanwasan, musammam ma matasan ciki," in ji Slot.