'Kama Tukur Mamu ba zai hana ceto sauran fasinjojin jirgin kasa ba'

An wallafa

Gwamnatin Najeriya ta ce kama Tukur Mamu, mai shiga tsakanin nan a kokarin sakin fasinjojin jirgin kasan da aka sace, ba zai kawo cikas ga yunkurin da gwamnatin kasar ke yi na kubutar da sauran fasinjojin da suka rage a hannun 'yan bindiga ba.

Ministan kula da harkokin 'yan sanda na kasar Mohammed Maigari Dingiyadi ne ya bayyana haka jim kadan bayan kammala taron majalisar tsaro ta kasa da aka yi a Abuja ranar Alhamis.

“Ina ganin masu maganar sun san Mamu ne kawai ba su san sauran masu sulhu ba tsakanin hukumomi da ƴan fashin.

“Akwai mutane da dama da ke sa baki kuma maganganun suna amfani,” in ji Ministan Tsaron, a hirarsa da BBC bayan kammala taron.

Jami'an 'yan sandan kasa da kasa ne suka kama Tukur Mamu ranar 7 ga watan Satumba a Masar, sannan kuma aka dawo da shi Najeriya bisa umarnin gwamnatin tarayya inda aka mika shi hannun jami’an 'yan sandan farin kaya na DSS.

Ya ƙara da cewa “Akwai ƴan uwan mutanen da hukumomin tsaro da ke shiga tsakani a lamarin. Kama Mamu ba zai kawo ƙarshen sulhun ba.”

Me ya sa aka kira taron?

Dama an saba duk wata ake gabatar da irin wannan taro na tsaro a ƙasar, kuma Dingyaɗi ya ce na wannan karon an yi shi ne don tattauna irin ci gaban da aka samu a kawo karshen matsalolin rashin tsaro a kasar.

Ya ce kuma ga irin bayanan da aka samu daga su shugabannin sassan tsaro na wannan kasar shi ne an samu cikakken ci gaba, “kuma mun gamsu da irin ci gaban da ake samu, kuma shugaban kasa ya yaba wa su shugabannin sassan na tsaro.”

Ministan ya ce an kuma nemi shugabannin tsaron da su ci gaba da wannan kokari da ake yi na kai hari wuraren da ƴan ta’adda ke zaune.

“In sha Allahu ƴan Najeriya za su ci gaba da ganin ci gaban da ake samu, kuma kamar yadda na fada wannan ci gaba ba wai a kan tebur kawai muke ganinsa ko a rahotannin da muke samu ba, a a har da jaridu da kafafen yada labarai ma sun shaidi cewa akwai wannan ci gaba da ake samu.

“Sannan su ma ƴan Najeriya masu bin hanyoyin da abubuwan suka tsananta sun shaidi ci gaba da aka samu don a yanzu suna tafiya lafiya a titunan,” ya ƙara da cewa.

Minista Dingyaɗi ya ce hakan ya danganci tsare-tsare da salo da gwanintar yadda za a fuskanci lalura.

“Kullum su hukomomin tsaro suna sabunta salo da dabarun, kuma muna ganin wannan mataki da aka dauka yanzu ya yi alfanu kuma ya kawo ci gaba,” in ji shi.

Mece ce matsayar gwamnati kan samar da ‘yan sandan jihohi?

A baya-bayan nan ana ta samun ƙaruwar kiraye-kiraye kan samar da tsarin ƴan sandan jihohi a Najeriya.

Ko a farkon wannan mako ma sarakunan gargajiya da gwamnonin arewacin ƙasar sun nuna son samar da tsarin ƴan sandan jihohin a wani taro da suka yi.

A wajen taron tsaron na ranar Alhamis, ministan ya ce tsarin mulkin ƙasa ya bai wa kowa damar fadin albarkacin bakinsa, “Kuma gwamnati jama’a take yi wa aiki, kuma tana sauraren abubuwan da jama’a ke fada.

“Iya saninmu dai a yanzu abin da muke da shi ‘yan sanda kawai na gwamnatin tarayya ne, amma jama’a idan suna son ƴan sandan jihohi sun san hanyoyin da za su bi su same su.

“Su je majalisar tarayya su gabatar da hujjoji kuma wakilansu su ɗauka su yi muhawara a kansu. Idan ya karbu a hukumance, ba abin da gwamnatin tarayya za ta iya illa ta tabbatar da shi,” kamar yadda ya ce.

Ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ba ta taɓa adawa da abin da mutane ke so ba.

“Idan abin da jama’a ke so kenan gwamnatin tarayya a shirye take hannu biyu ta karbi abin da jama’a ke bukata.

“Jama’a ne suka kawo gwamnatin nan kuma jama’a take yi wa aiki,” in ji ministan.