Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rabe ya kasa buge Autan na Aisha a damben gasar Maraba
Rabe ya kasa ɗaukar fansa a kan Autan na Aisha a damben da suka buga a safiyar Lahadi a Marabar Nyanya da ke jihar Nasarawa a Najeriya.
Sarkin yakin masu gidajen damben Najeriya, Idris Ɓamɓarewa ne ya saka ladan naira 100,000 ga 'yan wasan biyu ga mai rabo.
Turmi uku suka yi ba kisa, inda Rabe Shagon Ebola ya yi korafi cewar ɗan damben Guramaɗa ba ya kai dambe sai zagaye fili kawai ya iya.
Shi kuwa Autan na Aisha ya ce ai da hakan ne ya buge ɗan wasan Kudun a can baya da suka dambata, ya ce an kawo masa 'yan dambe da yawa a duk mako, amma har yanzu yana tsaye.
Mako uku da ya wuce Autan na Aisha ya buge Rabe Shagon Ebola a damben gasar a Marabar Nyanya.
Ɗaya wasan na 100,000 shi ma tashi aka yi ba kisa tsakanin Ɗan Aliyu da Garkuwan Yahayan Tarasa.
Turmi uku suka buga, inda Ɗan Aliyu daga Arewa ya yi ta ƙoƙarin yin dambe shi kuwa Garkuwan Yahaya ya yi ta gudu yana fita daga da'irar filin.
Wannan shi ne karon farko da aka dambata tsakanin Ɗan Aliyu daga Arewa da Garkuwan Yahayan Tarasa daga Guramaɗa.
Kafin nan an buga wasa 12, waɗanda suka kayatar.
Damben da ya yi kisa:
- Bahagon Ali Yaro ya buge Dogon Inda
- Shake Garkuwan Dunan bata jemu ba ya doke Shagon Basiru
- Mabilu ya ɗauki fansa a kan Shagon Dogon Messi
- Shagon Babangida ya yi nasara a kan Ɗan Bichi
- Dogon Maiduguri ya doke Shagon Autan Makaɗa
- Da wanda Shegun ya buge Shagon na Aisha
Wasannin da aka yi canjaras:
- Dogon Aleka da Autan Makaɗa
- Shagon 'Yar biyat da Tulo Shagon Tuwo
- Boloko da Shagon Lawwali
- Shage Garkuwan Duna da Shagon Lawwali
- Ushu Shagon Inda da Shagon 'Yar biyat
- Shagon Boka da Shagon Kurma