Dan Najeriya Awoniyi ya zama mafi tsada da Nottingham ta saya

An wallafa

Nottingham Forest ta dauki dan kwallon tawagar Najeriya, Taiwo Awoniyi daga Union Berlin a matakin wanda ta saya mafi tsada a tarihin kungiyar.

Mai shekara 24, ya amince da kunshin kwantiragin kaka biyar kan fam miliyan 17, wadda za ta buga Premier League a kakar da za a fara cikin watan Agusta.

Awoniyi ya ci kwallo 20 a karawa 43 a kakar da aka karkare ta bana, kuma shi ne na farko da Forest ta dauka, tun bayan da ta samu tikitin buga babbar gasar tamaula ta Ingila.

Dan kwallon tawagar Najeriya, wanda ya buga wasannin aro a Union Berlin ta mallaki Awoniyi daga baya a Yulin 2021 daga Liverpool, wadda ya fara taka leda a matakin kwararre.

Bai yi wa Liverpool wasa ko daya ba, tun bayan da ta dauke shi a 2015, wanda ya yi ta zuwa buga wasannin aro a kaka shida da ya yi a kungiyar Anfield.

Bayan da ya ci kwallo 15 a wasa 31 a lik, Awoniyi shi ne na shida a zura kwallaye a raga a Bundesliga, wanda ya kai Union Berlin mataki na shida a teburi.

Hakan ne ya sa kungiyar za ta buga gasar Zakarun Turai ta Europa League a bana a karon farko tun bayan kakar 2001-02.

Tun bayan da ya fara buga wa Super Eagles tamaula cikin watan Oktoba, kawo yanzu Amoniya ya yi karawa hudu da cin kwallon farko a fafatawa da Sudan a Janairu a gasar kofin Afirka a Kamaru.

Forest na sa ran daukar aron mai tsaron raga, Dean Henderson, mai shekara 25 daga Manchester United a kakar nan, tana kuma tattaunawa da mai tsaron bayan Mainz, Moussa Niakhate, mai shekara 26.