Mazauna Funtua da kewaye na kokawa kan yawaitar hare-haren ƴan bindiga

..

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Mazauna garin Funtua da kewaye a Jihar Katsina a Najeriya na kokawa game da yawaitar harin da ƴan bindiga ke kaiwa a yankin, waɗanda kuma suke satar mutane domin neman kudin fansa.

A cewar wasu daga cikin jama'ar yankin, tun ƴan bindiga suna musu ɗauki ɗai-ɗai, yanzu lamarin ya munana, kasancewar a ranar Alhamis ɗin da ta wuce kusan mutum goma aka kwashe a lokaci guda.

Mazauna kewayen birnin na Funtua sun bayyana cewa ƴan bindiga sun saka su a gaba inda suke kai masu hari suna garkuwa da mutane.

Jama'ar garin sun ce tun suna tsammanin samun sauki zuwa wani lokaci, lamarin sai ta'azzara yake yi har ta kai ga wasu ala tilas sun fice daga matsugunansu.

Wani mazaunin yankin na Funtua ya ce akwai wasu ƙauyuka da ke kewayen Funtua wadanda tuni suka tarwatse saboda bala'in ƴan bindiga.

Ya kuma ce akwai wasu ƙauyuka kamar irin su Zagamawa, su ma jama'ar garin duk sun tashi, sai dai jama'ar garin su je cikin Funtua su kwana da safe kuma su koma.

Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Jihar Katsina ta ce tana da labarin abubuwan da ke faruwa a Funtua da kewaye amma ta ce jami'anta na ɗaukar mataki.

Kakakin rundunar SP Gambo Isa ya bayyana cewa sakamakon yadda daji ke kara duhu a lokacin damina, dama ƴan bindiga na yawan zafafa hare-harensu amma ya ce jami'ansu suna iyakar bakin kokarinsu.

Haka kuma kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa kwamshinan ƴan sandan jihar da kwamandojin sojoji da sauran hukumomin tsaro da ke jihar sun dukufa wajen hada kai tare da tsara dabarun tunkarar lamarin. Lamarin tsaro na ci gaba da tabarbarewa a kewayen Funtuwa, har ta kai ga mutanen yankin sun fara zanga-zanga domin nuna rashin jin dadinsu.