Abubuwan da ya kamata ku sani kan raba jadawalin Euro 2024

An wallafa

Kasashen Turai za su san makomarsu a gasar Europ 2024 ranar Lahadi, lokacin da za a raba rukuni da misalin karfe 11:00 a Franfurt.

Cikin kasashe 55, 53 ne za a raba, yayin da mai masaukin baki Germeny za ta samu gurbi na kai tsaye, ita kuma Rasha aka cire ta saboda mamayr da ta yi wa Ukraine.

Kasashe 12 ciki har da Scotland sun samu damar buga wasan cike gurbi a wasannin Nations League.

Wasannin Nations League da ake bugawa a kusa sun nuna manyan kungiyoyin nahiyar, yayin da Ingila ta fita daga cikin tukunyar farko.

Ingila da Wales da Scotland duka na rukuni na biyu, yayin da Northern Ireland ke tukunya ta biyar ko ta shida.

Ta yaya ake raba rukuni?

Za a raba rukunai bakwai ne da kasashe biyar - sannan rukuni uku da kasashe shida ciklinsu. Sannan kasashe hudun da suka je wasan kusa da na karshe a Nations League da suka hada da Croatia da Netherlands da Italy da kuma Spain - za a raba su zuwa wasu kananan rukunnai.

Sannan kungiyoyi biyun sama a kowanne rukuni cikin 10 za su samu tikitin Europa 2024 kai tsaye.

Germany ta samu damar zuwa kai tsaye saboda ita ce mai masaukin baki, yayin da sauran kasashe ukun za su zo ne ta hanyar wasan cike gurbi na Nations League.

Za a fara raba rukunin ne daga 23 ga watan Maris zuwa 21 ga watan Nuwamba na 2023.

Su waye a cikin tukunyar?

Tukunyar Nations League (Manyan da za a raba zuwa kananan rukunnani): Netherlands, Croatia, Spain, Italy.

Tukunya ta 1 (sauran manyan kasashen): Denmark, Portugal, Belgium, Hungary, Switzerland, Poland.

Tukunya ta 2: France, Austria, Czech Republic, England, Wales, Israel, Bosnia-Herzegovina, Serbia, Scotland, Finland.

Tukunya ta 3: Ukraine, Iceland, Norway, Slovenia, Republic of Ireland, Albania, Montenegro, Romania, Sweden, Armenia.

Tukunya ta 4: Georgia, Greece, Turkey, Kazakhstan, Luxembourg, Azerbaijan, Kosovo, Bulgaria, Faroe Islands, North Macedonia.

Tukunya ta 5: Slovakia, Northern Ireland, Cyprus, Belarus, Lithuania, Gibraltar, Estonia, Latvia, Moldova, Malta.

Tukunya ta 6: Andorra, San Marino, Liechtenstein.

Akwai abubuwa da dama da suka hana a hada wasu kasashe a guri daya.

Wasu dalilan siyasa sun sa za a raba Armenia da Azerbaijan, kamar yadda za a raba Belarus da Ukraine da Gibraltar da Spain.

Kosovo ba zai yiwu ta hadu da Bosnia-Herzegovina ko Serbia a wuri daya ba.

Kasashen yankin Baltic da na Nordic biyu ne kawai za a rika hada wa cikin rukuni guda saboda matsanacin sanyi.

Saboda yankunan da Kazakhstan da Azerbaijan da kuma Iceland ke ciki na makurar yankunan Turai - yasa ba za a iya hada su wuri guda ba.