Tambayoyin da suka shafi kwata fainal a Champions League

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Ranar Laraba aka kammala wasannin zagayen 'yan 16 a Champions League, an samu takwas da za su ci gaba da karawar daf da na kusa da na karshe.

Ga jerin tambayoyi da amsoshi da suka shafi Champions League.

Wacce rana za a raba jadawalin kwata fainal a Champions League?

Za a raba jadawalin zagayen quarter finals ranar Juma'a 17 ga watan Maris a hedikwatar UEFA a Nyon a Switzerland.

Wadanne kungiyoyi ne suka kai daf da na kusa da na karshe?

Bayern Munich daga Jamus

Benfica daga Portugal

Chelsea daga Ingila

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Inter (daga Italiya

Man City daga Ingila

Milan daga Italiya

Napoli daga Italiya

Real Madrid daga Sifaniya

Ko kungiyoyi daga kasa daya za su kara da juna a quarter final kuwa?

E haka ne jadawalin a bude yake kowa zai iya haduwa da kowacce kungiya ce koda daga kasa daya suke, kuma koda sun hada a rukuni ne.

Ko jadawalij da za a yi zai hada da wasannin daf da na karshe?

Haka ne - za a raba jadalin zuwa gida uku, wanda zai shafi hada kungiyoyin da za su fafata a zagayen daf da na kusa da na karshe.

Na biyu kuwa za a fayyace yadda kungiyoyin za su kece raini a daf da karshe ga dukkan hudun da za su kai zagayen gaba.

Na uku kuwa za a fidda kungiyoyin da za su zauna a gida don karbar bakuncin wasannin farko da wadanda za su kai ziyara.

Ta yaya za a raba jadawalin daf da na kusa da na karshe a Champions League?

Nan gaba ne Uefa za ta sanar yadda za ta bi ta gudanar da jadawalin daf da na kusa da na karshe.

Yaushe za a fara wasannin quarter finals?

Za a fara buga wasannin farko ranar Talata 11 da kuma Laraba 12 ga watan Afirilu.

Za kuma a kece raini a wasa na biyu tsakanin 18 da kuma 19 ga watan Afirilu.

Yaushe za a buga wasannin daf da karshe?

Za a fara wasan farko a daf da karshe daga ranar 9 da 10 ga watan Mayu, sannan a buga zagaye na biyu ranar 16 da 17 ga watan Mayu.

Yaushe za a buga karawar karshe?

Za a buga wasan karshe ranar Asabar 10 ga watan Yuni.

A ina za a buga wasan karshe a Champions League na bana?

Za a buga wasan karshe ranar 10 ga watan Yunin 2023 a Istanbul a filin wasa Ataturk Olympic Stadium.

A filin ne AC Milan ta ci Liverpool kwallaye daga baya kungiyar Anfield ta farke ta lashe kofin a kakar 2005.