Yanzu me ya rage wa ƙasar da ta damƙa tsaronta a hannun Wagner?

An wallafa

Yayin da Mali ke yaƙar mayaƙa masu iƙirarin jihadi da 'yan a-ware, ta mayar da lamuran tsaron ƙasar kacokam a hannun sojojin hayar Wagner.

Sai dai yanzu an tabbatar da mutuwar shugaban sojojin hayar, dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya kuma na ficewa, sannan Mali na fuskantar matsaloli.

Ma'aikacin BBC Feras Kilani ya ziyarci wani yankin sahara mai hatsari a arewacin ƙasar - dan jaridar duniya na farko da ya ziyarci yankin a bara - domin ganawa da mutanen da rikicin ya rutsa da su.

Dare ya yi sosai lokacin da muka kafa tantinmu, muka kunna wuta domin girka abincin darenmu da itace, sannan muka baje bargunanmu, don ɗora haƙarƙarinmu, muka yi a rigingine a hasken wata da taurari.

Ba da jimawa ba, ƙarar wani babur ya katse yanayin tsit da muka shiga a cikin saharar.

A kusa da mu, na jiyo ana ta ɗana bindiga tsakanin maza da ke ɗauke da makamai a cikinmu. Muna tare da wata tawagar 'yan a-waren Buzaye, waɗanda suka faɗa wa mutumin da ke kan babur cewa ya wuce.

Tafiyarsa ke da wuya, wanda ya karɓe mu ya ce lokaci ya yi mu ma mu tafi nan take.

Akwai hatsari mu ci gaba da zama da shi, ganin yana cikin masu leƙen asiri ga ƙungiyar da ake alaƙantawa da al-Qaeda.

Mun kasance cikin yanayin taka-tsantsan, muka sauya wandunan jeans da ke jikinmu zuwa tufafin gargajiya da kuma sanya irin rawanin buzaye domin sajewa da su, saboda idan aka gano akwai baƙi a wannan sansani, to zai iya ankarar da mayaƙan cewa ga mu nan kuma ana iya garkuwa da mu.

Mun tattara kayanmu cikin hanzari muka fara tuƙi cikin duhu, ba tare da kunna fitilar mota ko tocilan ba saboda gudun abokan rakiya.

Wannan yankin na arewacin Mali ya fi ƙarfin ikon gwamnati, kuma ƙungiyoyin 'yan a-waren Buzaye da mayaƙa masu iƙirarin jihadi da ake alaƙantawa da al-Qaeda - ba su da kyakkyawar alaƙa tsakaninsu, amma dai sun cimma jituwar cewa kada wani ya takura wa ɗan'uwansa.

Tashin hankali da fargabar da muka shiga a wannan dare sun nuna yanayin tsananin rikici da ƙasar take ciki yayin da suka tunkari wata gaɓa mai hatsari.

Gwamnati ta juya baya ga dakarun wanzar da zaman lafiya, tare da dogaro a kan mayaƙan Wagner domin samar da tsaro.

Amma yanzu, an tabbatar da mutuwar shugaban mayaƙan, Yevgeny Prigozhin, a wani hatsarin jirgin sama, inda ake diga ayar tambaya a kan ayyukan mayaƙansa da fargabar halin da Mali za ta iya tsintar kanta.

Tserewa daga IS

A ɓangaren gabas, mayaƙan IS sun ƙaddamar da kansu kuma suna ƙoƙarin kare yankuna masu yawa da suka mamaye.

Muna son mu gana da fararen-hula da suka maƙale sakamakon rikicin da mayaƙan IS suka haddasa. Sai mun yi tafiyar kilomita dubu ɗaya a cikin sahara domin kai wa birnin Kidan da ke gabashin Mali.

Lokacin da muka isa, mun iske sansanonin da dubban 'yan gudun hijira ke rayuwa, bayan sun tsere daga gidajensu.

''Mayaƙan IS na yawan zuwa nan,'' kamar yadda Fatima ta faɗa mana, zaune a ƙasa cikin tantinsu - sun rataya kwalaye a sassan mashimfiɗinsu. Shekararta 60 kuma a yanzu nan ne matsugunninta, tare da 'yarta da jikokinta biyu da ke zaune a kusa.

An kashe mijinta da surukinta lokacin da mayaƙan IS suka kai hari ƙauyensu.

''Sun kashe duk wani namji a garin, kuma sun ƙone duk kayan abincinmu da dabbobi,'' a cewarta.

Wasu sun ba mu irin wannan labarin na yadda aka lalata musu kayan abinci, dabbobi, tare da barin su cikin talauci.

Galibin ƙananan yaran da muka gani babu riga a jikinsu ballantana takalmi.

Fatima, da sauran abin da ya rage musu a dangi, sun yi tafiyar ɗaruruwan kilomitoci domin isa Kidal daga tsohon gidansu na jihar Menaka a gabashin Mali.

Kamar yadda ya kasance a kanmu, mun sha wahala sosai a tafiyar da muka yi a sahara.

Babu hanya mai kyau, duk inda muka ratsa, sahara ce muke ta faman ketawa a motocinmu. Wasu lokutan mukan ci karo da bishiyoyi da tarin tsirrai.

Al'ummar Kidal na cikin mawuyancin hali, amma dai suna rayuwa.

"Mun gano ruwa da makwanci, don haka sai muka tsaya," a cewar Fatima.

Mutanen da ke zaune a wannan sansani na samun taimakon kayan buƙatun yau da kullum daga ƙungiyoyi ba da agaji, amma dai tallafin ba ya isa.

Mun yi kiciɓis da Musa Ag Taher, ɗaya daga cikin mazan da ke wannan sansani.

Mayaƙan IS sun kai hari gidansa.

"Lokacin da IS suka shiga garin sai na binne kai na har zuwa lokacin da suka fice, sannan na yi dabara na tsere tare da iyalina," a cewarsa.

Ya kuma bayyana yadda ya haƙa rami mai zurfi tare da rufe kansa da ƙasa don ɓoye kansa. Ya yi ƙoƙarin tserewa tare da 'ya'yansa huɗu.

Komawa ga Wagner

Duk da yake, Kidal ya fi tsaro a kan yankin da Fatima da Musa suka baro, amma akwai fargabar al'amura za su sake rincaɓewa.

A 2012, sojoji sun kitsa juyin-mulki, yayin da 'yan tawaye da mayaƙan IS suka ƙwace iko da yankin arewaci, tare da ayyana cikakken 'yanci.

Sabuwar gwamnatin riƙon-ƙwarya ta bukaci sojojin Faransa su zo su yaƙi mayaƙa masu tsattsauran ra'ayin addini. Watanni bayan isar su a 2013, Majalisar Ɗinkin Duniya ta aika dakarunta na wanzar da zaman lafiya da ake kira Rundunar Minusma.

Shugaban sojojin ƙasar ya kwace iko a 2020 - tun wannan lokacin sojojin da suka yi juyin-mulki suka nesanta kansu da Faransa, ƙasar da ta yi musu mulkin mallaka, daga bisani sojojin Faransa sun fice sun bar ƙasar.

A 2021, gwamnati ta gayyaci mayaƙan Wagner zuwa Mali, domin su taimaka mata da tsaro kuma ba da jimawa ba, sojojin hayar na Rasha suka kasance su kaɗai ne ke bai wa ƙasar taimakon soji daga waje.

Gwamnati ta buƙaci dakarun wanzar da zaman lafiyar Majalisar Ɗinkin Duniya dubu goma sha biyu su fice - yanzu haka suna gab da barin ƙasar gaba ɗaya.

Mun ziyarci sansanin Majalisar Ɗinkin duniya da ke Kidal wanda ake shirin rufewa a watan Nuwamba.

An jibge buhunan yashi tare da amfani da wayoyin ƙarfe masu kaifi wajen yin katanga, kewaye da sansani saboda tsaro.

Daga nesa, kana iya hango mutane sanye da hular kwano ruwan ɗorawa da fararen ababen hawa jere ɗauke da tambarin MDD.

Masu gadi a bakin ƙofar shiga sansanin sun kira wani a wayarsu ta oba-oba, sai kwatsam mutum uku suka bayyana.

Suka ce mu daina naɗar bidiyon da muke yi tare da shaida mana cewa akwai mutanen da ke shirin tafiya, kuma ba za mu iya tattaunawa da su ba.

Mazauna yankin na nuna fargabar cewa idan dakarun MDD suka fice, za su bar giɓin da IS za ta iya kankanewa, mayaƙa masu alaƙa da al-Qaeda da 'yan a-ware duka na gumurzun ƙwace iko.

Ana kiyasta cewa akwai sojojin Wagner 1,000 a Mali - adadin da bai kai kashi ɗaya cikin 100 na dakarun MDD da za su maye gurbinsu ba, kuma akwai fargabar ayyukansu ko ƙarfinsu, ba zai iya yaƙar ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi ba.

A farkon wannan shekara, MDD ta zargi Wanger da aikata muggan laifuka tare da sojojin Mali, suna mai bayyana yanayin cin zarafi mafi muni da suka aikata, ga mutanen da suke kashewa, su binne a manyan kaburbura, kuma suna azabtarwa da aikata fyaɗe da lalata a yanki Mopti.

An kuma bayyana yadda sojojin Mali, da mayaƙan Wagner ke horarwa, suka kashe mutane akalla 500, galibinsu fararen-hula da ba sa riƙe makamai a ƙauyuka.

Gwamnatin Mali ta musanta aikata wani laifi.

A wani yanki, mun riske wata ƙungiya ta 'yan a-ware daga ƙabilar Buzaye da ke kiran kansu da suna Kidal.

Sun nuna damuwar cewa gwamnatin Sojin Mali, da ke iko da yankin kudancin ƙasar, na iya ƙoƙarin ƙwace abin da ya rage da sunan sansanin MDD inda dakarun ƙetare suka fice. Ya ce wannan na iya sake buɗe sabon babin yaƙi.

"Idan dakarun Minusma suka ba da waɗannan sansanoni ga sojojin Mali, Minusma ce za ta ɗauki alhakin duk abin da ya biyo baya,'' a cewar Bilal Ag Sharif, shugaban Buzaye na yankin, a tattaunawar da na yi da shi.

''Gwamnatin Mali ita ma laifi zai hau kanta, saboda tana neman abin da bai dace ba, kuma ba za mu amince da hakan ba,'' a cewarsa, yana mai jadadda cewa ƙungiyar ba za ta amince da ƙwace ikon yankin ba.

Duk da ƙoƙarin samar da tsaro, sansanonin 12 na MDD a sassan Mali ya samar da ayyuka dubu 10. Sun yi hayar masu fassara, direbobi, da mutanen da suke rabon abinci da wasu ayyuka kamar samar da wuta a hanyoyi da wasu buƙatun lafiya.

''Za a bar waɗannan mutanen babu aiki, babu wata madogara, babu wata hanyar samun kuɗi domin ciyar da iyalansu,'' a cewar Sharif. Ya damu matuƙa cewa mayaƙa masu iƙirarin jihadi za su kutsa domin cin moriya.

''Wannan zai bai wa ƙungiyoyin jihadi sabbin damammaki na hayar mayaƙa,'' a cewarsa.

A sansanin 'yan gudun hijirar, mun iske yadda yara suka jeru a ƙasa suna ɗaukar darasi.

Wani malami riƙe da bulala yana karanto ayoyin Kur'ani, su kuma suna bi.

Mayaƙan ISIS sun kashe iyayensu, kuma ana iya ganin irin hatsarin da suke ciki da kuma barazanar mayaƙa su dauke su a matsayin sojin haya.

Manufar Rasha

Kwarin gwiwar da mayakan Wagner ke nunawa a yankin ya kasance abin diga ayar tambaya, duk da hakan. Gwamnatin Amurka ta zargeta da tafiyar da harkokin zinare da mahakar diamond a wasu yankunan Afirka, suna mai cewa mayaƙe ne da ke rikita komai, burinsu ko manufa ita ce azurta kai da albarkatun ko dukiyar kasashen.

Kwanaki kalilan kafin haɗarin jirgin Rasha, an ga Yevgeny Prigozhin a wani faifai bidiyo yana ikirarin yana Afirka.

BBC ba ta iya tabbatar da inda aka naɗi bidiyon ba, amma acikinsa, Prigozhin na cewa kungiyarsa na bude kofa ga '''yancin Afrka'', kuma Wagner na binciken albarkatun kasa da kuma yakar kungiyoyin jihadi da sauran miyagun mutane.

A wajen birnin Kidal, mun ziyarci wani yanki da ake harkar zinare a Mali. Dan karamin wuri ne, babu wani tsaro sosai, sai dai ana ta harkar hako ma'adinai da narkasu da hannu.

Amma da daruruwan irin wannan wurare a kasar, Mali na iya fitar da tan 60 ne kacal a shekara na zinare, inda ta kasance kasa ta biyar a Afirka da ke fitar da wannan albarkatu.

Ƙabilar Buzaye na nuna matukar damuwa cewa sojojin Wagner za suyi kokarin kwace musu masana'antunsu da suke harkar zinare. Kuma muddin hakan ya faru a cewar Sherif to za a zub da jini.

Barazanar yanki

Majalisar Dinkin Duniya, MDD t ayi gargadin cewar barazanar da ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi ke haifarwa na ƙaruwa a sassan Mali da Nijar da Burkina Faso a shekarar da ta gabata.

Dukkan ƙasashen uku sun fuskanci juyin-mulkin sojoji, inda aka hamɓarar da gwamnatin farar-hula a Burkina a 2022, a Nijar cikin watan Yulin bana.

Yanzu dai akwai rashin tabbas kan makomar Wagner, don haka akwai tababa kan makomar Mali da ci gaba da dogaro kan Wagner domin tsaron ƙasar. Idan abubuwa a ƙasar suka ci gaba da taɓarɓarewa, hakan zai kasance babban ƙalubale da haifar da rashin zaman lafiya a yankin.